Yan Sanda a Kano Sun Sake Matsaya kan Zargin Ta'addanci, Sun Gano Wani Shiri a Maulidi
- Rundunar 'yan sandan Kano ta janye matakin hana Mauludin Tijjaniyya bayan takaddama mai karfi da gwamnatin jihar ta yi kan lamarin
- Gwamnatin Kano ta zargi 'yan sanda da yunkurin hana taron shekara-shekara da ake shiryawa tun shekaru 39 da suka gabata
- Rundunar 'yan sanda ta gargadi jama’a game da wasu barayi da ke fakewa da aikin cajin wayoyin salula domin aikata sata a wurin taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kano - Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta janye matsayinta na hana gudanar da Mauludin Tijjaniyya da aka shirya yi a yau Asabar a jihar.
Rundunar yan sanda ta tabbatar da kasancewar jami'an tsaro a wurin taron domin ba da tsaro mai inganci da kare rayuka.

Source: Facebook
Gwamnatin Kano ta soki yan sanda kan maulidi
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ya biyo bayan takaddama da gwamnatin jihar inda ta zargi jami'an tsaro da yunkurin hana taron addini na shekara-shekara da aka saba yi.
Gwamnatin Kano ta gargadi 'yan sanda kan zama yan amshi shatan wasu da ba su ke son ci gaba da zaman lafiyar jihar.
Gwamnati ta yi zargin cewa jami’an tsaro na kokarin hana taron da aka saba gudanarwa tsawon shekaru 39.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta janye jami’an tsaro nan take domin barin taron ya gudana.
Wasu na zargin Gwamnatin Tarayya da neman hanyar kawo cikas a cikin Kano domin cimma wata manufa saboda biyan buƙatar kansu.
Yan sanda sun sake matsaya kan harin ta'addanci
'Yan sanda sun yi ikirarin cewa sun samu rahotannin sirri na yuwuwar harin ta'addanci a wuraren taruka a wasu sassan jihar.
Bayan haka, an tura jami’an tsaro zuwa filin wasa na Sani Abacha, inda za a gudanar da Mauludin Tijjaniyya na kasa.
Kiyawa ya kuma yi gargadi game da barayi da ke fakewa da aikin cajin waya domin aikata sata kusa da wurin taron.
“Kowa ya yi hattara! Muna nan don tabbatar da an gudanar da Mauludi cikin kwanciyar hankali. Allah ya kiyaye mu daga masu neman tada husuma."
“Wasu suna shirin kafa wuraren cajin waya kusa da wurin Mauludi, Manufarsu ita ce sata. Don haka, a yi hattara."
- Abdullahi Haruna Kiyawa
Yan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Tun farko, mun ba ku labarin cewa Rundunar ‘yan Sanda a Kano ta bayyana cewa ta samu rahoton sirri kan wasu ‘yan ta’adda da ake zargi suna shirin kai hari sassan jihar.
Jami'in hulda da jama’a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bukaci mazauna Kano su guji wuraren da ke da cunkoso domin kare kansu daga matsala.
SP Kiyawa ya tabbatar da cewa rundunar ta dauki matakan tsaro ta hanyar tura ƙwararru daga sassan kula da abubuwan fashewa yayin da ake shirin yin taron Maulidin Tijjaniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
