Babban Hafsan Tsaro Ya Fadi Shirin Bello Turji bayan Sojoji Sun Matsa Masa Lamba
- Babban hafsan tsaron Najeriya (CDS) Janar Christopher Musa ya bayyana cewa tantirin shugaban ƴan ta'adda Bello Turji na shirin miƙa wuya
- Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa dakarun sojoji sun hallaka mataimakin Bello Turji da wasu manyan kwamandojinsa
- Babban hafsan tsaron ya nuna cewa duk da shirin Bello Turji na miƙa wuya, mutane irinsa masu kashe bayin Allah bai kamata su ci gaba da rayuwa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban hafsan tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yi magana kan matsin lambar da sojoji suke yi wa Bello Turji.
Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa tantirin shugaban ƴan ta’addan, Bello Turji, ya nuna shirinsa na miƙa wuya ga jami'an tsaro.

Asali: Twitter
Janar Christopher Musa ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello Turji na shirin miƙa wuya
Babban hafsan tsaron ya bayyana cewa dakarun sojoji sun kawar da mataimakin Bello Turji da wasu manyan kwamandojinsa.
Janar Christopher Musa ya ce hakan ya sanya Bello Turji ya rabu da mafi yawan mutanen da ke ƙarƙashinsa, wanda hakan ke nuna alamar cewa yana da niyyar ajiye makamai.
"Su ƴan ta’addan suna cikin ƙauyuka mutane suna ganinsu. Don haka, wani lokacin yana kai kamar awa biyu bayan sun gansu kafin a samu labari. Don haka, lokacin da ka samu labarin kafin ka yi wani abu, ya bar wurin."
“Amma zan gaya muku, mun kawar da mataimakinsa na biyu, mun kawar da mafi yawan kwamandojinsa, yanzu haka an tilasta masa sakin mafi yawan mutanen da ke ƙarƙashinsa."
"Zan gaya muku cewa kwanan nan ya fara cewa ba ya son komai, ya shirya miƙa wuya."
- Janar Christopher Musa
Duk da batun cewa Bello Turji yana da niyyar miƙa wuya, babban hafsan tsaron ya jaddada cewa bai kamata a bar duk wanda ya kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba."

Kara karanta wannan
Shin da gaske an cafke dan ta'adda, Bello Turji? an samu karin bayani kan rade radin
"Muna son kawar da kowa. Duk wanda ya yi kisan kai ya kamata ya fuskanci hukunci, irin su bai kamata a bari su ci gaba da rayuwa ba."
- Janar Christopher Musa
Sojoji sun kashe makusantan Bello Turji
A ranar Laraba hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce sojojin rundunar Operation Hadarin Daji sun kawar da mataimakin Bello Turji mai suna Aminu Kanawa.
A wata sanarwa da daraktan watsa labarai na DHQ, Edward Buba, ya fitar, ya ce sojojin sun raunata wasu na kusa da shugaban ƴan ta'addan, ciki har da Dosso (ƙanin Bello Turji) da Danbokolo.
Edward Buba ya ce sojojin sun kawar da wasu manyan kwamandojin Bello Turji da suka haɗa da, Abu Dan Shehu, Jabbi Dogo, Dan Kane, Basiru Yellow, Kabiru Gebe, Bello Buba, da Dan Inna Kahon-Saniya-Yafi-Bahaushe, da sauransu.
Bello Turji ya sauya mafaka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Bello Turji ya sauya mafaka bayan dakarun sojoji sun matsa masa lamba da kai hare-hare a kwanakin nan.
Sahihan majiyoyi sun bayyana cewa an hango ɗan ta'addan a dajin Kalage da ke yankin Mashema a Kagara ta Gabas da ke jihar Zamfara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng