Yadda Abacha Ya Yi Dabara da Ya Gano Yunkurin Yin Garkuwa da Shi Lokacin Mulkinsa

Yadda Abacha Ya Yi Dabara da Ya Gano Yunkurin Yin Garkuwa da Shi Lokacin Mulkinsa

  • A shekarar 1997, Janar Sani Abacha ya tsallake yunkurin sace shi da aka shirya a Enugu, kamar yadda wani tsohon soja ya bayyana
  • Abacha ya gane manufar tafiyar kuma ya fasa tafiya zuwa Enugu, wanda ya hana nasarar yunkurin sauya gwamnatiron tilasta shi yin murabus daga mulki
  • Abacha ya gane manufar tafiyar kuma ya fasa tafiya zuwa Enugu, wanda ya hana nasarar yunkurin sauya gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Manjo Seun Fadipe (mai ritaya), tsohon dogari ga marigayi Laftanar-janar Oladipo Diya, ya magantu kan wata makarkashiya da suka shirya.

Fadipe ya bayyana yadda Janar Sani Abacha ya tsallake yunkurin sace shi da aka yi niyyar yi a jihar Enugu a shekarar 1997.

An gano yadda aka shirya sace marigayi Sani Abacha
Marigayi Sani Abacha ya tsallake yunkurin garkuwa da shi lokacin mulkinsa. Hoto: Contributor.
Asali: Getty Images

Muƙaman da marigayi Oladipo Diya ya riƙe

Kara karanta wannan

'Su bar kujerunsu': Atiku ga yan siyasa da ke sauya sheka, ya fadi hanyoyin gyara dimukraɗiyya

Channels TV ta ruwaito cewa Fadipe ya kasance dogarin Diya, wanda ya rike mukamin shugaban hafsoshin sojoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadipe ya yi magana kan marigayi Diya wanda ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 78 a duniya a wata ranar 26 ga watan Maris, 2023.

Marigayin kafin rasuwarsa ya rike muƙamin hafsan sojoji da kuma mataimakin Abacha yayin da yake mulkin Najeriya sannan ya mulki jihar Ogun.

A shekarar 1997 aka yanke masa hukuncin kisa bisa zargin cin amanar kasa amma ya kubuta bayan mutuwar Abacha.

Makarkashiyar da aka shirya wa Sani Abacha

Fadipe ya ce, Diya da abokan tafiyarsa sun shirya su sace marigayi Abacha a Enugu kuma su tilasta shi yin murabus, amma marigayin ya gane manufarsu.

"Akwai juyin mulki da aka shirya, ko da kuwa na jabu ne ko a'a, amma wannan shi ne matsalar da na samu da shugabana har ya mutu."

Kara karanta wannan

"Ana saye ra'ayin 'yan adawa da N50m": Atiku ya tona asirin gwamnatin Tinubu

"Da Abacha ya yi tafiyar, da an kama shi kuma an sauya gwamnati, amma ya gane hakan kuma ya hana faruwar abin."

- Cewar Manjo Seun Fadipe

An zargi tsofaffin sojoji da cin amana

Fadipe ya bayyana cewa da sun gudanar da yunkurin a Abuja, sun samu nasara, amma wata hanya ta sa Abacha ya soke tafiya duk da cewa an tura tawagar fara shirye-shirye.

A ranar 9 ga Disamba, 1997, Fadipe ya ce bayan ganawa da Diya, ya bayyana masa cewa akwai wani abu dake tafe, kuma daga baya aka tabbatar da yunkurin.

Daga baya, Fadipe da Diya sun shiga hannu tare da wasu fiye da 200 bisa zargin yunkurin juyin mulki, amma daga baya aka yafe musu a karkashin Abdulsalami Abubakar bayan rasuwar Abacha a 1998.

Yadda Tinubu ya fallasa sirrin marigayi Abacha

A baya, kun ji cewa Sanata Babafemi Ojudu ya bayyana yadda Bola Tinubu ya yi rikodin din wata tattaunawa da wani lauya kan sata da aka zargi Janar Sani Abacha da yi.

Kara karanta wannan

"Za mu gyara inda ya kamata": Shettima ya lissafa muhimman ayyukan gwamnatin Tinubu

Rikodin din ya bayyana yadda Abacha ya karkatar da kimanin Dala biliyan 5 zuwa asusun bankuna a kasashen waje, ciki har da Amurka, Birtaniya, da Switzerland.

Duk da hadin kan Tinubu wajen tattara bayanan, ya yi kokarin hana wallafa labarin, amma Sanata Ojudu ya dage har aka buga shi a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel