Harin Ta'addanci: Gwamnatin Kano Ta Saba da 'Yan Sanda, Ta Fadi Shirin da Ake Yi

Harin Ta'addanci: Gwamnatin Kano Ta Saba da 'Yan Sanda, Ta Fadi Shirin da Ake Yi

  • Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan gargaɗin da ƴan sanda suka yi kan barazanar kai harin ta'addanci
  • Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano ya zargi ƴan sanda da yunƙurin hana wani taron mauludi na ƙasa
  • Ya bayyana cewa ƴan sandan sun hana amfani da wurin taron mauludin ƙasa na Tijjaniya wanda aka kwashe shekaru ana gudanarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi magana kan gargaɗin da ƴan sanda suka yi kan yiwuwar kai harin ta'addanci a jihar.

Gwamnatin ta Kano ta zargi ƴan sanda da yunƙurin hana wani taron mauludi na shekara-shekara.

Gwamnatin Kano ta musanta batun 'yan sanda
Gwamnatin Kano ta zargi 'yan sanda da hana taron mauludi Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Gwamnatin Kano ta yi watsi da gargadin ƴan sanda

Jaridar Daily Trust ta ce kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya yi watsi da maganar da ƴan sanda suka yi kan barazanar kai harin.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano dai ta bayyana cewa ta samu rahotannin sirri game da wasu ƴan ta’adda da ake zargi suna shirin kai harin ta'addanci a wuraren taron jama’a da muhimman wurare a jihar.

Da yake mayar da martani, kwamishinan ya ce ƴan sanda sun hana amfani da wurin taron Mauludin ƙasa na Tijjaniyya, wanda ake gudanarwa duk shekara har tsawon shekaru 39.

“Kano, a matsayin cibiyar tarihi ta ilmin addinin Islama da zaman lafiya tsakanin addinai, za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan da ke inganta zaman lafiya da haɗin kai.”
“Wannan abun ba kawai ba shi da amfani ba ne, har ma da rashin dacewa, domin babu wani rahoto na barazanar tsaro a jihar Kano da zai sa a ɗauki irin wannan matakin mai tsauri."
"Kasancewar jami’an tsaro a wurin wannan muhimmin taro na addini bai kamata ba kuma ba abin da za a yarda da shi ba ne."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan cafke Muhuyi Magaji, sun fadi abin da ya faru

- Ibrahim Abdullahi Waiya

Gwamnatin Kano ta ja ƙalubalanci ƴan sanda

Kwamishinan ya bayyana cewa duk da matakin ƴan sandan suka ɗauka, za a ci gaba da gudanar da mauludin kamar yadda aka tsara a filin wasa na Kofar Mata.

Ya tabbatarwa masu sha’awar halartar mauludin cewa gwamnatin jihar ba za ta bari a samu wata tangarɗa ba.

“Za a gudanar da mauludin ƙasa na Tijjaniyya kamar yadda aka tsara daga ƙarfe 8:00 na safe a filin wasa na Kofar Mata."
"Wannan taron addinin wata ƙungiya mai rajista ce ta shirya shi, kuma duk wani yunƙurin hana shi zai zama take haƙƙin ƴan ƙasa na damar yin taro da gudanar da addininsu a Najeriya."

- Ibrahim Abdullahi Waiya.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta janye jami’an tsaronta daga wurin taron ba tare da ɓata lokaci ba, yana mai jaddada cewa filin wasa na Kofar Mata mallakar gwamnatin jihar Kano ne.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Ƴan sanda sun yi ram da ɗalibai a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta samu nasarar cafke wasu ɗalibai da suka kai hari kan wani malami a kwalejin fasaha ta jihar.

Ɗaliban dai sun shiga hannu ne bayan malamin ya kai ƙararsu a wajen ƴan sandan kan zargin yin unƙurin fille masa kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng