Oshiomhole Ya Cire Tsoro, Ya Faɗi Manyan Ƙasa Masu Hannu a Haƙar Ma'adanai na Haram
- Sanata Adams Oshiomhole ya ce an san janar-janar da suka yi ritaya da ke jagorantar haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba
- Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta ɗauki matakin soji a kansu don kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya
- Oshiomhole, tsohon shugaban APC na ƙasa ya ce a baya ya taɓa rubutawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wasika kan haka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Janar-Janar na rundunar sojojin Najeriya waɗanda suka yi ritaya suna da hannu a ayyukan haƙar ma'adanai ta haramtacciyar hanya.
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar dattawa, Sanata Adams Oshiomhole, ne ya bayyana hakan yau Juma'a a Abuja.

Source: Facebook
Oshiomhole ya yi wannan zargin ne yayin da shugaban kwamitin ma’adanai, Sanata Sampson Ekong, ya miƙa rahoton kasafin kuɗin 2025, Daily Trust ta kawo.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
Sanata Ekong ya mika rahoton ne ga kwamitin kasafin kudi na Majalisar dattawa wanda Sanata Oshiomhole ke matsayin mamba.
Janar-janar na rundunar soji suna da hannu
Adams Oshiomhole ya ce Najeriya ba za ta cimma nasara a ƙoƙarinta na raba tattalin arzikinta zuwa fannoni daban-daban ba idan ba ta dakatar da wannan ɓarna ba.
A cewar tsohon gwamnan Edo, dole gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta magance haƙar ma'adanai ba kan ƙa'ida ba idan tana son daina dogaro da mai kaɗai.
A kalamansa, tsohon shugaban APC Oshiomhole ya ce:
“Janar-janar da suka yi ritaya su ke jagorantar hakar ma’adanai ta haramtacciyar hanya a ƙasar na kuma mun san su ba ɓoyayyen mutane ba ne.
"Eh, mun san su, babu wanda zai ce bai san su ba, na rubuta wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wasiƙa kan wannan batu lokacin yana ofis.
“Na faɗawa Buhari ne saboda wata tawaga da na tura ta gudanar da zaɓen fidda gwani a wani wuri, ta dawo min da rahoton cewa babban kalubalen shirya zaɓen a Zamfara shi ne hakar ma’adanai ba bisa ƙa'ida ba.
Oshiomhole ya ba shawarar magance matsalar
Dangane da yadda za a kawo ƙarshen lamarin, Sanata Oshiomhole ya ce ya ba da shawarin amfani da ƙarfin soji wajen kawar da duk mai hannu a lamarin.
“Idan muna son magance wannan matsala, ya zama dole mu tura sojoji su kashe duk wanda ke da hannu kamar yadda muka yi wa masu haƙar mai.
"Ya kmata mu tura dakarun haɗin guiwa da suka kunshi ƴan sanda, sojojin ƙasa da na sama domin maganinsu gaba ɗaya," in ji shi.
Kwamitin ya goyi bayan hujjojin Oshiomhole, inda ya bukaci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan magance haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.
Sanata Ndume ya jinjinawa sojojin Najeriya
Kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya bayyanaa cewa Najeriya na bukatar ƙarin jiragen yakin sojoji domin murkushe ƴan ta'addan Boko Haram.
Sanata Ali Ndume ya ce sojojin Najeriya za su iya murkushe 'yan ta'adda amma suna bukatar karin kudade don bunkasa ayyukansu.
Asali: Legit.ng
