An Kama 'Yan Fashi da Makami da Suka Tare Hanya a Tsakiyar Kano
- Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami a tsakiyar birnin Kano
- An ruwaito cewa jami'an 'yan sanda sun kama wukake da wayar salula a hannun su bayan sun kai hari a Magwan Road
- Biyo bayan lamarin, rundnar 'yan sanda ta yi kira ga al’umma da su rika bayar da bayanai domin taimakawa wajen dakile masu laifi a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rundunar ’yan sanda a Kano ta yi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami a unguwannin Kano.
Wadanda ake zargin sun hada da Aminu Muhammad mai shekaru 28 daga Sabon Titi, Abubakar Aminu mai shekaru 24 daga Gaida Diga, da Mujahid Muhammad mai shekaru 23 daga Na’ibawa.

Asali: Facebook
Kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook tare da fadin matakin da za su dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kakakin rundunar ’yan sandan jihar, jami’an tsaro sun yi nasarar gano makamai daga hannun matasan da ake zargin.
Yadda aka kama 'yan fashi a Kano
'Yan sanda sun bayyana cewa an kama matasan ne sakamakon wani samame da suka yi a ranar 15 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.
Kakakin rundunar ya bayyana cewa 'yan dabar sun tare Magwan Road inda suka yi wa mutane fashi tare da karɓar wayoyinsu.
Bayan samun rahoto daga wani mutumin kirki, tawagar jami’an tsaro ƙarƙashin jagorancin CSP Aliyu Muhammad Auwal ta yi saurin daukar mataki, wanda ya kai ga cafke wadanda ake zargi.
Gudanar da bincike da tafiya kotu
A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu bayan kammalawa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya bayyana cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifuffuka ba.
A karkashin haka ya ce za su ci gaba da daukar matakai masu tsauri domin tabbatar da cewa jihar ta kasance cikin zaman lafiya.
Neman hadin kan jama’ar Kano
A jawabin da ya yi, CP Salman ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kasance masu ba da hadin kai ga rundunar ’yan sanda ta hanyar bayar da bayanai a kan masu aikata laifi.
Ya ce bayar da bayanai cikin gaggawa zai taimaka wajen dakile ayyukan masu laifi da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
An bayyana lambobin waya da za a iya tuntubar rundunar a yayin samun matsaloli ko kuma bayar da rahoton ayyukan barna:
- 08032419754
- 08123821575
- 09029292926
An kashe mataimakin Bello Turji
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta ce ta kai mummunan hari kan mayakan dan ta'adda, Bello Turji.
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka mataimakin Bello Turji da wasu tarin mayakansa da suka haura 20 a yankunan Zamfara da Sokoto.
Asali: Legit.ng