Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Fadi Amfanin 'Qur'anic Festival' ga Najeriya

Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Fadi Amfanin 'Qur'anic Festival' ga Najeriya

  • Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana goyon bayanta ga taron 'Qur’anic Festival' da aka shirya gudanarwa a Abuja
  • Sakataren majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce an shirya taron ne don haɗa kan Musulmin Najeriya da nuna baiwar ilimin Alkur’ani
  • Ya kara da bayyana yadda aka samo tunanin shirya taron, wanda tuni ya fara yamutsa hazo a tsakanin Musulmin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta bayyana dalilan goyon bayanta ga 'Qur'anic festival' da aka shirya yi a Abuja, ranar 22 Fabrairu, 2025.

Majalisar, ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bayyana cewa taron ya na matuka muhimmanci.

Musulmi
NSCIA ta dauki nauyin 'Qur'an festival' Hoto: Abdullahi Bala Lau/The Sultan of Sokoto TV
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta da jaridar Daily Trust, Sakataren Majalisar NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa bikin ba ya da wata manufa sai dai haɗa kan al’ummar Musulmi domin ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka samu tunanin bikin Alkur’ani

Farfesa Oloyede ya ce tunanin bikin ba daga wata ƙungiya guda ɗaya ya fito ba, amma wasu ƙungiyoyin Musulunci sun kawo ra’ayin ne ga majalisar, kuma an rungumi shirin.

Sakataren Majalisar ya ce:

“Ra’ayin ya fito ne daga ƙungiyoyin Musulunci, sannan Majalisar Kolin Musulunci ta Najeriya ta amince da cewa abu ne mai kyau a yi, wannan ya sa muka zama ɓangare na wannan al’amari wanda bikin ya shafi haɗa kan Musulmi."

Za a yi wa ƙasa addu’a a 'Qur’an festival'

Wani jami’in majalisar NSCIA ya ce 'Qur'anic festival' wani bangare ne na nuna kyakkyawan al’adun al’ummar Musulmi na ƙasar nan game da ilimin Alkur’ani.

Har ila yau, bikin na da nufin haɗa Musulmi a ƙarƙashin inuwa ɗaya domin nuna baiwar ilimin Alkur’ani da kuma inganta haɗin kai da zaman lafiya a ƙasar.

Jami'in ya kara da cewa:

“Mutane akalla 50,000 da suka haɗa da mahaddata, masu rubutu, masu karatun Alkur’ani da masu zanen kaligrafi daga sassa daban-daban na ƙasar nan da duniya za su halarci bikin,” in ji jami’in.

Kara karanta wannan

'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC

Ya kuma ce za a yi amfani da wannan dama domin yin addu’a ta musamman don samun zaman lafiya, dawwamar tsaro da bunƙasar ƙasa.

NSCIA ta karɓi ragamar 'Qur’anic festival'

An gano cewa shirin bikin ya samo asali ne daga ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida wa Ikamatus Sunna (JIBWIS) ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa na ƙungiyar, Sheikh Bala Lau.

Sai dai wata majiya a NSCIA ta ce yanzu majalisar ce za ta yi uwa da makarbiya wajen gudanar da taron saboda wasu dalilai.

Majiyar ta ce;

“Amma saboda damuwar tsaro da wasu batutuwa da suka shafi shiryawa, majalisar (NSCIA) ta ɗauki ragamar al’amuran domin ƙarfafa haɗin kai da wasu domin tabbatar da nasarar bikin.”

Jami’in ya kwantar da hankali kan batutuwan tsaro da suka shafi bikin, yana mai cewa shigar NSCIA cikin shirin na nufin tabbatar da tsaro.

JIBWIS ta yi magana a kan 'Qur'an festival'

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'a Wa Iqamatis Sunnah ta musanta zargin cewa an shirya taron mahaddata Alkur'ani domin tallata Bola Tinubu a zaben 2027.

Sheikh Dr. Ibrahim Idris, daya daga cikin shugabannin kungiyar, ya bayyana cewa taron da ake shirin yi ba na Izala ba ne, illa dai Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ce ke daukar nauyinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel