An Shiga Alhini bayan Rasuwar Tsohon Minista a Arewa, Gwamna Ya Yi Ta'azziya

An Shiga Alhini bayan Rasuwar Tsohon Minista a Arewa, Gwamna Ya Yi Ta'azziya

  • Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Janar Jeremiah Useni, ya rasu a yau Alhamis, 23 ga Janairu, 2025, bayan fama da jinya mai tsawo
  • Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga danginsa, Sojojin Najeriya, Jihar Filato, da kasa baki daya
  • Janar Useni ya yi ayyuka masu daraja a rayuwarsa, ciki har da jagoranci, siyasa, da kokarin tabbatar da zaman lafiya musamman a Arewacin Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jos, Plateau - Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni, ya rasu.

Dangin marigayin sun bayyana cewa ya rasu ne ranar Alhamis, 23 ga Janairu, 2025, bayan fama da doguwar jinya.

Tsoohn ministan Abuja, Useni ya riga mu gidan gaskiya
Gwamna Caleb Mutfwang ya yi jimamin mutuwar tsohon Ministan Abuja, Janar Jeremiah Useni. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gwamna Caleb ya fadi alherin marigayi, Useni

Rasuwar Janar Useni na kunshe a cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran Gwamna Caleb Mutfwang mai suna Gyang Bere ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Watanni da aure, diyar mataimakiyar gwamna ta yi bankwana da duniya yayin naƙuda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga danginsa, Sojojin Najeriya, Jihar Filato, da kasa baki daya.

Ya ce Janar Useni ya yi shugabanci na koyi kuma ya yi wa Najeriya hidima da kwazo ba tare da nuna son kai ba.

Useni ya yi kokari a zaman lafiyar Plateau, Arewa

Gwamna Mutfwang ya jaddada kokarin da Useni ya yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman a Arewacin Najeriya da Jihar Filato, abin da ba za a taba mantawa da shi ba.

Ya bayyana tarihin marigayin a matsayin wanda ya yi hidima ga Najeriya cikin kwarewa, ciki har da kasancewa Ministan Sufuri, Kwamanda a Sojojin Najeriya, da Ministan Abuja.

Bayan ya yi murabus daga aikin soja, Janar Useni ya shiga siyasa, inda ya ci gaba da hidima ga kasa.

Ya taba zama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ANPP da kuma Sanata mai wakiltar Yankin Filato ta Kudu a 2015 karkashin PDP.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya jajanta da Malamin Musulunci, yayan gwamna suka kwanta dama

Gwamna ya ce ba za a manta da Useni ba

Gwamnan ya yaba da rayuwar Useni mai cike da sadaukarwa, yana mai cewa ya bar kyakkyawan tarihi na tausayi, kirki, da jajircewa wajen inganta rayuwar al’umma.

Ya ce tarihin Jeremiah Useni zai ci gaba da zama abin tunawa ga wadanda suka san shi da ma wadanda za su samu tarihin sadaukar da rayuwarsa da ya yi.

“A madadin iyalina, gwamnati, da mutanen Jihar Filato, muna miƙa ta’aziyya ga Shugaban Kasa, Sojojin Najeriya, danginsa, da duk wadanda ke jimamin wannan babban rashi."

- Caleb Mutfwang

Dan kwamishinan yan sandan Abuja ya rasu

A baya, kun ji cewa dan kwamishinan ƴan sandan Abuja, Tunde Olatunji Disu ya mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2035.

Wannan rashi ya jefa rundunar ƴan sanda cikin jimami musamman saboda a ranar CP Disu ya je ta'aziyya gidan DPO na ofishin Ushafa wanda shi ma ɗansa ya rasu.

Kwamishinan ya yi ta'aziyya ga iyalan DPO bisa wannan rashi tare da fatan samun rahama ga wanda ya mutu da sauran wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.