'Yan Bindiga Sun Jefa Mazauna Benuwai a Tashin Hankali, Sun Kashe Mutane da Dama

'Yan Bindiga Sun Jefa Mazauna Benuwai a Tashin Hankali, Sun Kashe Mutane da Dama

  • Wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a kauyen Uzer da ke jihar Benuwai, inda suka kashe mutane takwas da raunata wasu da dama
  • Yankin gundumar Tombo ya kwashe sama da shekaru 20 yana fama da matsalolin tsaro, wanda har ya tilasta al’umma yin hijira
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin yayin da ta sanar da matakin da ta dauka bayan mummunan harin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - Wasu ‘yan bindiga da ake zargi sun kai mummunan hari kauyen Uzer, gundumar Tombo da ke karamar hukumar Gaambetiev a jihar Benue.

Kauyen Uzer yana kan hanyar Ayilamo-Tse Abi-Tse Ikyo-Tyulen, tafiyar mintuna huɗu kacal daga garin Ayilamo, wanda ya sha fama da hare-hare.

'Yan sanda sun tabbatar da harin da 'yan bindiga suka kai kauyen jihar Benuwai
'Yan bindiga sun kashe akalla mutane 8 a jihar Benuwai, 'yan sanda sun tabbatar da harin. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

An ce 'yan bindigar sun kai harin na baya bayan nan da misalin 8:00 na daren Laraba, lokacin da 'yan garin ke zaune a gidajensu, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Benuwai: 'Yan bindiga sun kashe mutane 6

Wani da ya tsallake rijiya ta baya baya, Terlumun Akombo, ya ce sun ji ƙarar harbin bindiga yayin da suke zaune a gidajensu.

Terlumun Akombo ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun bi duhun dare sun bude wuta kan mai uwa da wabi tare da kashe mutane shida.

Ya shaida cewa an tsinci gawarwaki shida, yayin da wata mace da ɗanta, waɗanda suka ji mummunan rauni, suka mutu daga baya a asibitin Ayilamo.

Wasu daga cikin wadanda aka kashe sun haɗa da Sir Matthew Tyôkighir, Misis Myangega, Ortamem Zwa Injo, Mista Emmanuel Sanka, da Misi Justina Ashe.

Gundumar Tombo na fama da rashin tsaro

Wani shaidar gani da ido, James Kumaga, ya ce jami’an tsaro sun samu labari daga Ayilamo, amma ‘yan bindigar sun tsere kafin su iso.

An ruwaito cewa yankin gundumar Tombo ya dade yana fama da matsalar tsaro saboda hare-haren makiyaya da suka tilasta wa mutane barin gidajensu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

An ce yanzu yankin Tombo, wanda ya ƙunshi garuruwan Mbakorya, Mbaya, Mbazaar, da Iwendyer, ya zama kufai saboda tsoron hare-haren ‘yan bindiga.

Mazauna Tombo sun nemi agajin gwamnati

Shugaban al’ummar yankin, Tyodue Aboh, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Benuwai da su samar da tsaro don manoma su koma gonakinsu.

Shugaban ofishin 'yan sandan Logo ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kuma ce an fara bincike kan harin.

A halin yanzu, ana shirye-shiryen yi wa waɗanda aka kashe jana’izar haɗin gwiwa, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wannan hari ya sake fito da matsalar rashin tsaro da ke addabar yankunan karkara a jihar Benuwai a fili, inda aka ji mazauna yankin na neman agaji.

Mazauna Benuwai sun fara gudun hijira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mazauna garin Akor da wasu ƙauyuka a Nzorov, karamar hukumar Guma, jihar Benuwai, sun fara barin gidajensu saboda tsoron 'yan bindiga.

Wannan ya biyo bayan kashe wani manomi, Terzungwe Shaku, da 'yan bindigar suka yi bayan ya kasa biyan kuɗin fansa Naira miliyan 20 da suka nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.