Ana Tsaka da Farautar Bello Turji, Tinubu Ya Fadi Tanadin da Ya Yiwa Sojojin Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa sojojin Najeriya cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu don jin daɗi da nasarar aikinsu
- Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da arikin sojojin Bola Tinubu a Abuja, wanda ya ƙunshi gidaje 614 da kayan more rayuwa
- Wannan na zuwa ne yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da tsananta kai hare-hare kan 'yan ta'adda da kara kaimi wajen farautar Bello Turji
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban Bola Tinubu ya tabbatar wa da sojoji cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa yin kasakasa a gwiwa wajen kula da jin daɗinsu ba.
Shugaban kasar ya yi alkawarin samar da duk wasu abubuwa da ake buƙata don sauƙaƙe aikin sojoji tare da inganta walwalarsu.

Source: Twitter
Alkawarin da Tinubu ya daukarwa sojoji

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Mai girma Bola Tinubu ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da sansanin barikin sojoji na Bola Tinubu da ke Abuja, inji rahoton Punch.
Tinubu ya ce:
"Sanin cewa gwamnatin tarayya na a shirya a kodayaushe domin samar da duk abubuwan da sojoji ke bukata zai taimaka wajen cimma nasarar yakokin da suke yi.
“Ku ne jarumanmu, muna godiya da sadaukarwar da kuke yi wa ƙasar nan don tabbatar da zaman lafiya da tsaro.”
Shugaban ya tabbatar da cewa:
“Ba za mu taba yin wasa da jin daɗinku ba. Za mu ci gaba da kashe kuɗi don inganta walwalarku.”
Tinubu ya nemi sojoji su kula da sabon barikin
Tinubu ya ƙara da cewa sadaukarwar sojoji abin a yaba ce, kuma "hanya ɗaya da za mu iya nuna hakan ita ce ta ci gaba da tallafa wa maza da mata da ke a cikin kakinmu."
Shugaban kasar ya umarci sojojin da su kula da gine-ginen barikin sojojin da aka kaddamar domin tabbatar da dorewar kayayyakin da zuba a ciki
“Cigaba da gyare-gyare tare da kula da abubuwan more rayuwa yana da muhimmanci wajen tabbatar da jin daɗin ma’aikatanmu,” inji Tinubu.
"Sojoji na fuskantar matsalar gidaje" - Olufemi
Shugaban sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nuna damuwa kan rashin isasshen gidajen zama ga sojoji, inda ya ce fiye da kashi 40 ba su da muhalli.
Laftanar Janar Olufemi ya ce:
“Lokacin da na karɓi ragamar jagoranci, na fahimci cewa matsalar rashin gidaje ita ce ta kasance babbar ƙalubale da sojojin Najeriya ke fuskanta.”
Ya bayyana cewa sansanin da aka ƙaddamar yanzu ya ƙunshi gidaje 614, waɗanda aka tsara domin zaman manya da ƙananan sojoji tare da iyalansu.
Sojoji sun yiwa Bello Turji kofar rago
A wani labarin, mun ruwaito cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da kudurinsa na kama fitaccen dan ta'adda, Bello Turji.
Ya bayyana za a kama Bello Turji nan ba da jimawa ba, "domin sojoji na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su kai ga nasarar wannan aiki."
Haka zalika, Janar Musa ya ce an cimma nasarar kawar da dukkanin kwamandojin Bello Turji, wadanda suka rika taimaka masa wajen gudanar da ta'addanci a Arewa.
Asali: Legit.ng
