Wani soja ya kashe kansa a barikin sojojin Abuja, ya ce a tambayi matarsa dalili

Wani soja ya kashe kansa a barikin sojojin Abuja, ya ce a tambayi matarsa dalili

A ranar Alhais ne Legit.ng ta wallafa labarin cewa samu gawar wani soja a barikin sojojin ta Gowon da ke birnin tarayya, Abuja, tare da alkawarin kawari kawo karin bayani da zarar sun samu.

Bayanan da Legit.ng ta samu na baya bayan nan sun gano cewa sojan, wanda aka bayyana cewa sunansa Adedapo, ya bar wani rubutu a jikin takarda a wurin da aka samu gawarsa.

Adedapo, wanda direba ne da ke aiki da sashen kasafi da tsare-tsare a hedikwatar rundunar soji ta kasa da ke Abuja, ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a jikin kugiyar fankar dakinsa da ke jerin dakunan rukunin 'F' a sashen gidajen Muhammadu Buhari da ke barikin sojoji ta Gowon.

Duk da har yanzu ba a san takaimaiman dalilin da yasa sojan ya yanke shawarar kashe kansa ba, takardar da ya bari ya nuna cewa Adedapo ya kashe kansa ne sakamakon samun sabani a tsakaninsa da matarsa a kan aikinsa.

A jikin takardar, Adedapo ya rubuta: "mene ne matsalar Rose da aiki na, haka rayuwar mata da miji ya kamata ta kasance? a tambayi Rose mene ne matsalar ta da aiki na."

Majiyar mu ta sanar da mu cewa an ajiye gawar marigayin a babban asibitin kasa da ke Abuja.

Har yanzu hukumar rundunar soji ba ta fitar da wani jawabi ba a hukumance dangane da samun gawar sojan, amma wata majiya ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel