Dogo Gide Ya Gwabza Fada da Mayakan Boko Haram, An Sheke 'Yan Ta'adda Masu Yawa

Dogo Gide Ya Gwabza Fada da Mayakan Boko Haram, An Sheke 'Yan Ta'adda Masu Yawa

  • Tantirin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya tsallake rijiya da baya bayan mayaƙan Boko Haram na ɓangaren Sadiku sun yi masa kwanton ɓauna
  • Dogo Gide ya bayyana cewa ya yi nasara kan ƴan ta'addan inda ya kashe aƙalla guda 20 daga cikinsu tare da ƙwato makamai
  • Dangantaka ɗai ta yi tsami ne tsakanin Dogo Gide da ƴan Boko Haram tun bayan da aka kashe masa ɗan uwansa a shekarar 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Hatsabibin shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, ya gwabza faɗa da mayaƙan Boko Haram.

Dogo Gide ya kashe mayaƙan Boko Haram guda 20 na ɓangaren Sadiku sannan ya kwace makamai masu yawa a hannunsu.

Dogo Gide ya kashe 'yan Boko Haram
Dogo Gide ya kashe mayakan Boko Haram Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dogo Gide ya fitar da bidiyo

A wani bidiyo da ya bayyana, an nuna Dogo Gide yana magana ga abokan hamayyarsa, yana iƙirarin samun nasara bayan ƙoƙarin kwanton-bauna da mayaƙan Sadiku suka yi masa.

A bidiyon, Dogo Gide ya nuna abubuwan da ya ƙwace, ciki har da bindigogi AK-47 guda 10, wayoyin hannu, da katin shaida da ake nuna alamun mambobin ƙungiyar.

"Sadiku da ƴan ƙungiyarsa sun yi mana kwanton-ɓauna, amma mun yi nasara. Mutum ɗaya ne kawai a cikinmu ya ji rauni, yayin da muka kashe aƙalla mutum 20 daga cikinsu."

- Dogo Gide

Ya kuma zargi ɓangaren Sadiku da munafunci, yana sukar su da kashe mata, yara, da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da sunan jihadi.

Dogo Gide na gaba mai zafi da ƴan Boko Haram

Gabar da ke tsakanin Dogo Gide da sassan Boko Haram, musamman ƙungiyar da Sadiku ke jagoranta, ta samo asali ne daga dalilan da suka shafi ɗaukar fansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

Bayanan sirri masu ƙarfi sun nuna cewa Dogo Gide, wanda ya taɓa zama abokin aikin Boko Haram, ya juya musu baya bayan kashe ɗan’uwansa Sani a shekarar 2023.

Tun daga wancan lokacin, Dogo Gide ya sha alwashin ɗaukar fansa kan mutuwar ɗan’uwansa, yana kuma aiki don korar mayaƙan Boko Haram daga yankin da yake iko da shi.

Ayyukan Gide na baya-bayan nan sun mai da hankali ne kan yankin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja, inda aka ruwaito cewa ya rushe shingen Boko Haram a kan hanyar Kuruba-Uduwa.

Yayin da yake magana da al’ummomin yankin, Dogo Gide ya nemi gafara kuma ya yi alƙawarin dawo da zaman lafiya, sannan ya ƙarfafa gwiwar mutanen da suka yi gudun hijira su koma gidajensu.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Kawuri a ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Ƴan ta'addan a yayin farmakin sun yi gumurzu da dakarun sojoji na tsawon lokaci, inda daga baya suka janye bayan jami'an tsaro sun ragargaje su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng