Buhun Shinkafa N55,000: An Samu Jihar Arewa da Ake Sayar da Kayan Abinci da Araha

Buhun Shinkafa N55,000: An Samu Jihar Arewa da Ake Sayar da Kayan Abinci da Araha

  • Farashin kayan hatsi ya fadi warwas a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina a ranar Laraba, 22 ga Janairu, kamar rahoto ya nuna
  • Bayanin farashin da aka samu ya nuna cewa shinkafa ta sauko zuwa N55,000, yayin da wake, gero, da dawa suma suka fadi kasa
  • Kasuwar Dandume dai tana ci ne sau uku a mako — Laraba, Asabar, da Lahadi, inda ake ganin faduwar farashin zai taimaki talakawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Farashin kayan abinci musamman ma hatsi ya sake faduwa kasa warwas a kasuwar garin Dandume da ke jihar Katsina.

Rahotonni sun bayyana cewa an samu saukar farashin kayan hatsi a ranar Laraba, 22 ga watan Janairun 2024, ranar da kasuwar ke ciki.

Rahoto ya yi bayanin yadda aka samu faduwar kayan abinci a wata kasuwar Katsina
An samu faduwar farashin hatsi a kasuwar Dandume da ke jihar Katsina a ranar Laraba. Hoto: Ibrahim M Bawa
Source: Facebook

Farashin hatsi ya karye a Katsina

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Wani rahoton Ibrahim M Bawa, da aka wallafa a shafin jaridar Katsina Daily News na Facebook, ya nuna cewa buhun shinkafa ya koma N55,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka kwatanta da farashin hatsi a sati biyu da suka gabata, an samu faduwar farashin sosai a kasuwar Dandume a jiya Laraba.

Duba farashin buhunan hatsi na ranar Laraba, 22 ga Janairu a kasuwar Dandume:

  • Farar masara - N50,000 zuwa N54,000
  • Jar masara - N50,000 zuwa N55,000
  • Jar dawa - N51,000 zuwa 55,000
  • Farar dawa - N50,000 zuwa N56000
  • Gero da maiwa - N67,000 zuwa N700
  • Waken soya - N70,000 zuwa N78,000
  • Samfarerar shinkafa - N55,000 zuwa N65,000
  • Tsabar shinkafa - N140,000 zuwa N160,000
  • Barkono kanana ɗan mintsi - N260,000 zuwa N280,000
  • Barkono dan miyere - N100,000 zuwa N110,000
  • Barkono dan kuyalo - N190,000 zuwa N200,000
  • Farin wake - N90,000 zuwa N105,000
  • Kalwa - N130,000
  • Alkama - N115,000
  • Kuɓewa busassa - N85,000

Rahoto ya nuna cewa kasuwar Dandume dai na ci a duk ranar Laraba, Asabar da kuma Lahadi, wanda ke nufin cewa tana ci sau uku a sati kenan.

Kara karanta wannan

Trump ya kafawa Saudiyya ƙahon zuƙa, an ji abin da ya jawo faɗuwar farashin mai

Abin da yawo faduwar farashin hatsi

A tattaunawarmu da masanin kasuwar hatsi a yankin Funtua, Abdulmumini Sani Maska, ya shaida mana cewa akwai dalilai da suka jawo faduwar farashin hatsi.

Abdulmumini Sani, wanda dillalin hatsi ne ga manyan kamfanonin sarrafa hatsi ya ce garuruwa da dama sun samu damar yin noma a 2023 sabanin shekarun baya.

"Akwai garuruwan da sun samu saukin hare-haren 'yan bindiga, don haka sun yi noma a daminar bara. Wannan ya sanya an samu hatsi mai yawa a kasuwanni.
"Sannan har yanzu ana fama da rashin kudi a hannun jama'a, dole 'yan kasuwa su karya farashi idan har sun son sayar da kayansu, ko su lalace a hannunsu."

- Abdulmumini Sani.

Ya ce akwai yiwuwar farashin hatsi ya kara sauka har zuwa lokacin da za a fara azumi, inda kuma ake tunanin farashin zai iya tashi.

"Kusan ya zama al'adar 'yan kasuwa, idan azumi ko sallah ko wani babban biki kamar kirsimeti ya zo, suna kara kudin abinci.

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

"Duk da haka, farashin ba zai yi wani tashin azo a gani ba, don mutane ba su da kudin saye, sannan yanzu ba daga kowanne dan kasuwa kamfanoni ke sayen hatsi ba."

- A cewar dan kasuwar.

Bude boda ya karya farashin hatsi a Neja

A wani labarin, mun ruwaito cewa farashin kayan abinci ya fadi a kasuwannin hatsi na jihar Neja saboda shigo da kaya daga Chadi, Ghana, Benin da Burkina Faso.

Shigo da hatsi ya jawo yalwatar kayan abinci a kasuwanni, lamarin da ake ganin zai shafi 'yan kasuwa, masu sayarwa, da manoma sosai.

Masu adana hatsi na fuskantar asara saboda cikar kasuwanni da buhunan hatsi yayin da kamfanoni suka koma sayen kayan da aka shigo da su daga waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com