Ganduje Ya Tuna Baya, Ya Fadi Yadda Ya Hana 'Yan Bindiga Zama a Kano

Ganduje Ya Tuna Baya, Ya Fadi Yadda Ya Hana 'Yan Bindiga Zama a Kano

  • Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi tsokaci kan hanyar da ya bi wajen hana ƴan bindiga samun wurin zama a Kano
  • Ganduje ya bayyana cewa ya gayyato sojoji domin su kula da dajin Falgore wanda hakan ya sanya aka kori ƴan bindiga daga yankin
  • Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya buƙaci jami'an da su shiga cikin dazuzzuka su kai hare-hare kan ƴan ta'addan da ke ɓoye a ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da shawara kan hanyar kawar da ƴan bindiga a ƙasar nan.

Abdullahi Ganduje ya nuna cewa akwai buƙatar ɗaukar matakai masu tsauri, musamman wajen fuskantar ƴan ta’adda da ke ɓoye a cikin dazuzzuka, don magance matsalar rashin tsaro.

Ganduje ya ba sojoji shawara
Ganduje ya bukaci a fatattaki 'yan bindiga daga dazuzzuka Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ce Ganduje ya ce hanyar kawo ƙarshen ƴan ta'addan ita ce mamaye dazuzzukan da suke ɓoyewa.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya ba da wannan shawarar ne lokacin da ya jagoranci kwamitin NWC na APC a ziyarar ta’aziyya ga gwamnan jihar Neja, Mohammed Umar Bago, kan fashewar tankar man fetur da ya auku a Dikko, ƙaramar hukumar Gurara.

AbdullahiGanduje ya yabawa gwamnan Neja

Ganduje ya yabawa Gwamna Bago kan ƙoƙarin da ya yi na tabbatar da zaman lafiya a Neja duk da faɗin ƙasa da kuma yawan dazuzzukan da ke cikin jihar.

Ganduje ya nuna damuwa kan yadda ake jira sai an kawo hari kafin ɗaukar matakin magance hare-haren ƴan ta’adda a jihohi daban-daban na ƙasar nan.

Ya tuna yadda ya samu nasarar shawo kan ƴan ta’adda a dajin Falgore a jihar Kano a lokacin mulkinsa a matsayin gwamna.

Yadda Ganduje ya kori ƴan bindiga a Kano

Ganduje ya ce ya roƙi sojoji domin maida dajin wurin horaswa, wanda hakan ya kawar da dukkanin ayyukan laifi a yankin.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

"Mun zo nan don yi wa abokinmu, ɗan’uwammu, da al’ummar jihar Neja addu’a, muna ta’aziyya ga gwamna da al’ummar jihar Neja, iyalan waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka ji raunuka"
"Muna godiya da yadda kake kula da zaman lafiya a jihar Neja, saboda jihar Neja tana da yawan faɗin ƙasa mafi girma a ƙasar nan kuma tana da yawan dazuzzuka, wanda hakan na buƙatar ƙoƙari sosai wajen kiyaye zaman lafiya."
"Mai girma gwamna, mafita ga wannan matsala ita ce mamaye dazuzzukan. Ƴan ta’adda suna cikin dazuzzukan nan, me ya sa za mu tsaya jira maimakon ɗaukar matakin kai hari?"
"Lokacin da nake gwamnan jihar Kano, na roƙa ta hannun gwamnatin tarayya cewa sojoji su ɗauki nauyin kula da Dajin Falgore."
"Sojoji sun gina wurin horaswa a can, wannan ne ya taimaka wajen korar ƴan ta’addan daga wannan daji, kuma Kano ta samu zaman lafiya."

- Abdullahi Umar Ganduje

Ganduje ya yi magana kan takara a 2027

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan raɗe-raɗin da aka kan cewa zai yi takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Ganduje ya bayyana musanta shirin yin takarar inda ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng