Zaman Kotu Ya Gamu da Tangarɗa da Yan Bindiga Suka Kai Farmaki, An Kashe Fitaccen Lauya

Zaman Kotu Ya Gamu da Tangarɗa da Yan Bindiga Suka Kai Farmaki, An Kashe Fitaccen Lauya

  • An rufe kotuna a wurare uku a jihar Imo sakamakon kisan gillar da wasu ƴan bindiga suka yi wa fitaccen lauya, Chinedu Nwowu ranar Laraba
  • An ruwaito cewa miyagun sun tilastawa lauyan tsayawa yana cikin tafiya a mota, suka harbe shi har lahira nan take a garinsu
  • Babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda amma kungiyar NBA ta kira taron gaggawa kan lamarin yau Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Imo - An garkame kotunan da ke yankin Mgbidi, Oguta da na yankin Omumma a j.ihar Imo, ba za su fito zaman shari’a ba a ranar Alhamis,

Kotunan sun yanke hukunci kauracewa zaman shari'a ne sakamakon kisan gilla da aka yi wa Chinedu Nwowu, wani shahararren lauya a jihar a Imo.

Taswirar jihar Imo.
Lauyoyi sun fusata da aka yi wa abokin aikinsu kisan gilla a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Rahoton The Nation ya ce rufe kotunan na wucin gadi wani mataki ne na girmamawa da nuna adawa da kisan wannan lauya da aka yi a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindiga sun kashe lauya a Imo

An samu labarin cewa maharan sun yi wa lauyan kwanton bauna sannan suka harbe shi a garinsu, Mgbidi, da yammacin ranar Laraba.

Wani daga cikin abokansa ya bayyana cewa:

“Wasu mutane dauke da bindiga suka tare motar marigayin sannan suka harbe shi har lahira.”

Wannan lamari ya jefa jama’a a jihar Imo cikin tsoro da fargaba domin hukumomi ba su bayyana dalilin kisan lauyan ba har kawo yanzu.

Kungiyar lauyoyi (NBA) ta nuna damuwa

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen Orlu ya sanar da kauracewa zaman kotu a ranar Alhamis a yankunan Mgbidi, Oguta, da Omumma.

Ƙungiyar ta ɗauki wannan matakin ne domin karrama abokin aiki ma'ana lauyan da aka kashe, Chinedu Nwowu da kuma adawa da kisan gillar da aka masa.

Tuni dai NBA a Orli ta kira taron gaggawa domin tattauna wannan kisan da aka yi wa abokin aikinsu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Lauyoyi sun shiya zama kan kisan abokinsu

Sanarwa da Chukwuemeka Okoro ya fitar a madadin reshen kungiyar NBA na Orlu ya bayyana cewa za a gudanar da taron gaggawa da karfe 10 na safe a ɓabbar kotun Mgbidi.

“Bayan kisan gilla da aka yi wa ɗaya daga cikinmu, Chinedu Nwowu, a daren jiya a garinsu, Mgbidi, muna sanar da dukkan lauyoyi na Oru/Oguta cewa za a yi taron gaggawa mai muhimmanci yau da karfe 10:00 na safe a kotun Mgbidi.
"Babu zaman kotu a babbar kotun Magbidi, Oguta da Omumma, don haka muna rokon don Allah kowa ya zo taro da wuri."

An rufe kotu kan kisan lauya a Imo

Shugaban reshen Orlu na NBA, Ben Amukamara, ya ce ƴan kungiyar suna ganawa a Babbar Kotun Mgbidi a safiyar Alhamis domin tattauna kan kisan lauyan.

Ya kuma tabbatar da cewa babu kotun da za ta yi zaman shari’a a Oguta, Mgbidi, da Omumma sakamakon wannan kisan gilla, kamar yadda rahoton Vanguard ya kawo.

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya suka fada bayan Buhari ya yi kyautar daloli

Sojoji sun yi arangama da ƴan ta'adda a Imo

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun gwabza da wasu ƴan ta'adda ake kyautata zaton mayaƙan kungiyar IPOB ne watau ESN.

Yayin kazamin artabun da aka yi, sojoji guda biyu sun rasa rayukansu a jihar Imo da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262