Tinubu Ya Amince da Raba Naira Biliyan 4 ga Gidajen Talakawa Miliyan 10
- Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da tallafin kuɗi har Naira biliyan 4 ga mabuƙata a Najeriya daga watan Fabrairu zuwa Afrilu na 2025
- Tallafin zai amfani gidaje miliyan 10 da suka fi fama da matsaloli, musamman waɗanda suka rasa matsugunansu a yankin Arewa maso Gabas
- Gwamnatin ta ƙara amincewa da rancen Naira biliyan biyu mara ruwa ga manoma a ƙauyuka domin ƙara samar da abinci da dogaro da kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin bayar da tallafin kuɗi na Naira biliyan 4 ga gidaje mabuƙata a Najeriya domin rage raɗaɗin matsalolin talauci da ake fama da su.
Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwada ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da wani shirin tallafi a Abuja.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa an kaddamar da shirin ne a ginin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe za a raba tallafin N4bn?
Shirin bayar da tallafin kuɗin zai fara aiki daga watan Fabrairu zuwa Afrilu na 2025, inda za a tallafa wa iyalai da suka rasa matsugunansu, musamman a yankunan Arewa maso Gabas.
Farfesa Yilwada ya bayyana cewa shirin yana da nufin sauƙaƙa raɗaɗin da mutane ke fuskanta, musamman mata masu ciki, wadanda suka rasa mazajensu, da masu buƙata ta musamman.
Ministan ya ce;
“Shugaban ƙasa ya amince da bayar da tallafin kuɗi ga gidaje miliyan 10 da aka tantance su a matsayin waɗanda suka fi buƙata.
"Wannan zai taimaka wajen rage wahalar rayuwa ga gidaje masu fama da matsalolin rasa wajen zama da bala’o’i.”
Shirin raba rance ga manoma
Bugu da ƙari, gwamnatin ta amince da tallafin rance mara kudin ruwa na Naira biliyan 2 ga manoma a yankunan karkara.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027
Wannan tallafin zai kasance tsakanin N300,000 zuwa N400,000 ga kowanne gida, domin ba manoma damar samun kayan aikin gona da damar kasuwanci.
Farfesa Yilwada ya ce;
“Shirin rancen zai taimaka wa manoma wajen samun damar samar da abinci da kuma dogaro da kai.”
Manufar gwamnati kan matsalolin jin kai
Gwamnatin ta ce shirin raba tallafin na da nufin rage radadin talauci a ƙasar nan, musamman a wannan lokacin da ake fama da matsalolin tattali.
Ministan ya bayyana cewa an tsara shirin ne domin magance matsalolin jin kai musamman a jihohin Borno, Adamawa, Yobe da sauran yankunan da rikice-rikice suka shafa.
A ƙarshe, an yi kira ga jama’a da su rungumi wannan dama tare da tabbatar da amfanin da za a samu daga shirin.
Abba ya raba tallafin N2.3bn a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya raba tallafin dabbobi ga mata domin dogaro da kai.
Rahoton Legit ya nuna cewa gwamnatin ta musa cewa awaki kawai aka saya da makudan kudi har N2.3bn, inda ta bayyana yadda aka kashe kudin.
Asali: Legit.ng