Za a Yi Hadaka da China domin Noma Dukkanin Filayen Jihar Nasarawa
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana burinsa na ganin an amfana da kowace kasar noma domin habaka tattali da wadatar da abinci
- Abdullahi Sule ya yi bayani kan yadda zai aiwatar da tsarin noma ta amfani da kayan zamani a kowanne yanki na jihar Nasarawa
- Wata tawagar 'yan kasuwa daga kasar China ta nuna sha'awarta kan hadin gwiwa domin bunkasa noman zamani da gwamnatin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi A. Sule, ya sha alwashin ganin an amfana da kowane fili da za a yi noma a jihar.
An ruwaito cewa hakan na cikin burin gwamnan na bunkasa aikin gona da samar da arziki ga al’umma.

Source: Facebook
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin wata tafiya da ya yi zuwa kasar China.

Kara karanta wannan
An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Sule ya koka kan rashin noma
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana damuwarsa kan yadda jihar ke da filaye masu yawa, wadanda suka dace da noma, amma ana barin su a banza ba tare da yin amfani da su ba.
A cewar gwamnan, hakan babban cikas ne ga cigaban jihar Nasarawa da tattalin arzikin al’umma.
Abdullahi Sule ya bayyana haka ne yayin wata doguwar tafiyar jirgin kasa daga lardin Henan zuwa Nanchang, a kasar China.
A yayin tafiyar, gwamnan ya ce tsarin noman zamani zai taimaka wajen bunkasa noma da ci gaban jihar Nasarawa.
Tsarin noman zamani a Nasarawa
A cikin wata hira da ya yi da wata tawagar ‘yan kasuwa a kasar China, Gwamna Sule ya yi nuni da yadda za a yi amfani da kwarewa wajen tantance iri da ya dace da kowane yanki na jihar.
Abdullahi Sule ya ce;
“A kullum ina fatan ganin ana amfani da kowane filin noma a jihar Nasarawa kamar yadda muka gani a kasar China.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Ya kara da cewa rarraba manyan injunan noma da irin shuka zuwa kananan hukumomi a jihar wani bangare ne na tabbatar da kudurin gwamnatinsa na bunkasa nomam zamani.
Hadin gwiwa da 'yan kasuwar China
Shugaban tawagar ‘yan kasuwa daga kasar China, Mista Chen Qiang, ya yaba da hangen nesan gwamna Sule na bunkasa noma a jihar Nasarawa.
A cewar Chen Qiang;
“Kasar China za ta yi alfahari da yin aiki tare da jihar Nasarawa domin bunkasa aikin noma wajen amfani da injunan zamani.”
Chen Qiang ya kara da cewa ya fahimci cewa filayen jihar Nasarawa sun fi wasu filaye a kasar China kyau, saboda haka suke son yin amfani da damar domin samar da ci gaba a jihar.
Tawagar ta kunshi wasu fitattun shugabannin kamfanoni daga kasar China kamar Zheng You, Shugaban Tongyi Group, da Chen Xiaoping, wanda ya yi aikin fassara a yayin tattaunawar.
Ana ganin cewa ziyarar wata dama ce ta karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin jihar Nasarawa da China.
'Yan China za su koyar da noma a Jigawa

Kara karanta wannan
'Ni kadai ke da iko': Gwamnan APC ya rikita zaman makoki, ya gargadi maciya amana
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa ya kai wata ziyara kasar China da niyyar bunkasa harkar noma.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa zai hada kai da kamfanin kasar China domin koyar da dabarun noman zamani ga al'ummar Jigawa.
Asali: Legit.ng