Kungiyoyin Dalibai Sun Watsa wa Tinubu Ƙasa a Ido bayan Shirin Raba Masu Shinkafa

Kungiyoyin Dalibai Sun Watsa wa Tinubu Ƙasa a Ido bayan Shirin Raba Masu Shinkafa

  • Shugabannin daliban jami'ar ABU da OAU sun yi watsi da tallafin shinkafa da gwamnatin Bola Tinubu ta ba su
  • Daliban sun bayyana cewa wannan ba zai magance matsalolin ilimi da ya dabaibaye manyan makarantu ba
  • Gwamnatin tarayya ta ware buhunan shinkafa biyu ga shugabannin kowace jami'a, kwalejin fasaha da ta kimiyya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugabannin Kungiyar Dalibai na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, Kaduna, da na Obafemi Awolowo (OAU), Ile-Ife, Osun, sun yi watsi da tallafin shinkafar gwamnati.

Gwamnatin tarayya, a karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta raba wa shugabannin Kungiyoyin Dalibai (SUG) na manyan makarantun kasar nan tallafin shinkafa.

Tinubu
Dalibai sun yi watsi da tallafin Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa Shugabannin Kungiyar daliban manyan makarantun biyu sun bayyana dalilansu na kun karbar buhun shinkafar da aka ba su a Abuja.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalibai sun yi watsi da tallafin Tinubu

Shugaban kungiyar daliban ABU, Ibrahim Nazeer, ya yi watsi da tallafin shinkafa yana mai cewa ba zai karbi kasonsa ba sai idan ya tabbata cewa za a ba sauran daliban jami'arsa.

Shugaban daliban ya kara da cewa;

“Ba zan karɓi tallafina ba sai an haɗa da isasshen tallafi ga sauran daliban ABU. Ina son bayyana cewa zan karɓi tallafin kawai idan ya kasance akwai isasshe don dalibanmu da yawa; in ba haka ba, ba zan karɓa ba,”
"Maimaikon raba shinkafa lokaci-lokaci, muna kira ga gwamnati ta mai da hankali kan samar da yanayi da zai bai wa mutane damar mallakar kayan bukatarsu, kamar shinkafa, da kansu.”

Daliban Kudu sun ki karbar shinkafar Tinubu

Shugaban daliban OAU, Damilola Isaac, ya ce bai karɓi tallafin shinkafar da aka gayyace su Abuja su karba ba, kuma ba zai karɓa ba ko da an kai masa ita har gida. Ya shawarci gwamnati a kan ta fi mayar da hankali wajen kawo ci gaba ga tsarin ilimi da walwalar dalibai, maimakon amincewa da tallafin da ba zai magance matsalolin ilimi ba.

Kara karanta wannan

Ana rade radin sauke Ganduje daga shugaban APC bayan Tinubu ya ba shi mukami

Gwamnatin Tinubu ta ware wa dalibai shinkafa

Gwamnatin tarayya ta ware buhu biyu na shinkafa mai nauyin kilo 25 ga kowanne shugaban kungiyar dalibai na jami’o’i, kwalejin ilimi, da kwalejin kimiyya da fasaha.

Hadimin Shugaba Tinubu kan Harkokin Dalibai, Asefon Sunday, ya bayyana cewa an gayyaci shugabannin dalibai biyu daga kowacce shiyya zuwa Abuja don karɓar tallafinsu.

Ya kuma kara da cewa ba zai yiwu gwamnati ta raba shinkafa ga dukkan daliban Najeriya ba, don haka aka zabi shugabannin dalibai su amfana da tallafin.

Gwamnatin Tinubu ta fusata NLC

A wani labarin, kun ji cewa Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi Allah-wadai da karin kudin kira ga 'yan Najeriya da gwamnatin tarayya ta amince da shi, wanda ya kai 50%.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa wannan matakin ya nuna rashin kulawa ga jin dadin al'ummar Najeriya, kuma ya nemi a dakatar da karin har sai an tattauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng