Dakarun Sojojin Sama Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Bindiga, an Soye Miyagu Masu Yawa
- Ƴan bindiga da ke ɓoye a dajin Alawa na jihar Neja sun ga ta kansu bayan dakarun sojojin sama sun yi musu ruwan wuta
- Dakarun sojojin sun kai hare-hare ta sama kan maɓoyar ƴan bindigan da ke cikin dajin, inda suka yi nasarar kashe miyagu masu yawa
- Hare-haren sojojin sama sun kuma yi sanadiyyar lalata wurin ajiye kayan aiki na ƴan bindigan bayan an jefa musu bam
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi ruwan wuta kan ƴan bindiga a jihar Neja.
Dakarun sojojin sun yi nasarar kashe ƴan bindiga masu yawa tare da lalata sansanin kayan aikinsu a dajin Alawa, da ke ƙaramar hukumar Shiroro.

Asali: Getty Images
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin sama sun jefa bama-bamai kan ƴan bindiga
Dakarun sojojin sun gudanar da farmakin ne a ranar 21 ga watan Janairu, bayan samun sahihin bayanan sirri da suka tabbatar da kasancewar ƴan bindiga a cikin dajin.
Ƴan bindigan suna da hannu a wasu munanan hare-hare, ciki har da kai harin bam a ranar 19 ga Disamba, 2024, a Bassa, ƙaramar hukumar Shiroro, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan fararen hula da dama.
Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya bayyana cewa farmakin, an sanya masa sunan Konan Daji.
Ya ce farmakin ya kasance wani ɓangare na kai hare-hare ta sama na tsawon kwanaki uku domin rage ƙarfin ƴan bindigan tare da hana su samun mafaka.
“An tura jiragen yaƙi don kai hare-haren sama a maɓoyar ƴan bindiga da aka gano a cikin dajin."
"Waɗannan hare-haren sun yi sanadiyyar kashe ƴan bindiga da dama da kuma lalata wurin ajiye kayan aikinsu, wanda aka tabbatar ta hanyar fashe-fashen da suka auku a sansanin."
- Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa
Sojoji na ƙara ƙaimi wajen fatattakar ƴan bindiga
Rundunar sojojin sama ta Najeriya ta jaddada ƙudurinta na ci gaba da ragargazar ƴan bindiga tare da da haɗin gwiwar sojojin ƙasa don tabbatar da tsaron al’ummomin jihar Neja da yankunan da ke makwabtaka da su.
Sojojin na ci gaba da ƙara ƙaimi wajen tsabtace dajin Alawa daga barazanar ƴan bindiga tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Wannan aikin ya ƙara haskaka jajircewar sojojin wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
Hukumomin tsaro sun buƙaci al’ummar yankin su ci gaba da ba da hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani motsi na ƴan bindiga domin tabbatar da ɗorewar nasarorin da ake samu.
Sojoji sun daƙile harin ƴan ta'addan ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun.sojojin Najeriya sun samu nasarar daƙile harin ƴan ta'addan ISWAP a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sojojin sun yi musayar wuta da ƴan ta'addan waɗanda suka so kai harin ta'addanci a cikin garin Gaidam na jihar Yobe.
Jami'an tsaro sun sheƙe wasu daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai, yayin da ragowar suka tsere.
Asali: Legit.ng