Bayan Kisan Matarsa, Ɗansa, Malamin Musulunci Ya Yi Addu'ar Allah Tsine, Ya Zargi Gwamnati
- Malamin addinin Musulunci a garin Owo, Alhaji Abdulkareem Adedokun, ya yi addu’ar la’ana kan ‘yan kungiyar asiri da suka kashe matarsa da dansa
- Rikicin kungiyar asiri ya yi sanadin mutuwar mutane hudu, ciki har da matarsa da dansa, wanda ya faru a Owo ranar 6 ga Janairu, 2025
- Gwamnatin Ondo ta sanya dokar hana fita daga maraice zuwa safiya, yayin da 'yan sanda suka kama mutane 19 da ake zargin suna da hannu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Akure, Ondo - Wani malamin addinin Musulunci a garin Owo, da ke jihar Ondo ya yi addu’ar la’ana kan wadanda suka kashe matarsa da kuma dansa.
Malamin mai suna Alhaji Abdulkareem Adedokun, ya shiga damuwa kan kisan matarsa, Temitope Adedokun, da dansa, Abdulmalik Adedokun.

Asali: Facebook
Yadda aka hallaka matar malami da ɗansa
Limamin ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook yayin da yake jimamin rashin a rikicin kungiyar asiri da ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin wanda ya faru ranar 6 ga Janairu, 2025 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane hudu.
Daga cikinsu akwaimatar limamin da kuma dansa, yayin da rikici tsakanin kungiyoyin asiri ya rikide zuwa tashin hankali.
Kokarin da gwamnatin Ondo ta yi kan lamarin
Biyo bayan lamarin, Gwamnatin Jihar Ondo ta sanya dokar hana fita daga maraice zuwa safiya, sannan ‘yan sanda sun tabbatar da cafke mutane 19 da ake zargin suna da hannu.
A rubutun da ya yi, malamin ya bayyana bakin cikinsa da fushinsa, inda ya labarta yadda aka kai hari kan matarsa a shagon ta.
Rubutun, mai taken “Wasika a bude ga mutanen karamar hukumar Owo da kewayenta,” ya bayyana damuwarsa da takaici kan yadda aka kashe matarsa da dansa.
Malamin Musulunci ya koka da kisan iyalinsa

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
“Na, Imam Alhaji Abdulkareem Adedokun, ina amfani da wannan dama domin sanar da jama’a abinda ‘yan kungiyar asiri a Owo suka yi min."
"Miyagun sun yi mani asara ta hanyar kashe matata da dana a ranar 6 ga Janairu 2025 inda suka shiga shagon matata, suka kashe ta da danta."
“Abin bakin cikin shi ne yadda ‘yan siyasa suka fara wasa da rayukan matata da dana, duk da cewa babu wani na daga cikin iyalanmu da ya taba shiga kungiyar asiri."
- Alhaji Abdulkareem Adedokun
A karshe, ya yi addu’ar la’ana kan masu hannu a lamarin da kuma wadanda ke boye su, tare da yin fatan Allah ya saka wa wadanda suka yada labarin.
Malamin Musulunci ya yi sha'awar mulkin Buhari
Mun ba ku labarin cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada, ya magantu kan shirye-shiryen zaben 2027, yana jan hankalin al'umma kan abin da ke tafe.
Malamin ya koka kan yadda ake kokarin tallata Bola Tinubu a zaben 2027, yana fadin cewa Allah ya tarwatsa masu wannan shiri.
A cikin wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, malamin ya ce Allah ya taimaki masu nufin alheri, ya kuma magance masu son tada fitina.
Asali: Legit.ng