Yobe: Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'addan ISWAP, Sun Ragargaji Miyagu

Yobe: Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Ta'addan ISWAP, Sun Ragargaji Miyagu

  • Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi yunƙurin kai harin ta'addanci a garin Gaidam na jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Dakarun sojoji na rundunar Operation yaƙi sun samu nasarar daƙile harin na ƴan ta'addan bayan an daɗe ana artabu
  • Bayan fatattakar ƴan ta'addan, jami'an tsaro sun kwaso makaman da tsagerun suka gudu bari bayan sun sha ruwan wuta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Sojojin sashe na biyu na rundunar Operation Hadin Kai sun yi nasarar daƙile wani hari da ake zargin mayaƙan ISWAP suka kai a garin Gaidam da ke jihar Yobe.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Talata, lokacin da mayaƙan ISWAP suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin garin daga yankin gabas.

Sojoji sun dakile harin 'yan ISWAP a Yobe
Sojoji sun fatattaki 'yan ISWAP a Yobe Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Zargin neman cin hanci daga jami'o'i: Dan majalisa ya fadi yadda abubuwa suka kaya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'addan ISWAP

Bayan hango mayaƙan, dakarun sojoji sun ɗauki matakin gaggawa inda suka yi musayar wuta wacce ta kwashe kimanin sa'o'i biyu.

Ƙoƙarin da sojojin suka yi ya tilastawa ƴan ta’addan janyewa, wanda hakan ya hana su shiga garin tare da cutar da mazauna yankin.

A safiyar ranar Talata, bayan gudanar da bincike a inda aka yi artabun, sojoji sun gano alamun jini a wurin, wanda ke nuna cewa akwai waɗanda suka ji rauni ko kuma suka mutu daga cikin ƴan ta’addan da suka tsere.

Haka kuma, dakarun sojojin sun gano bindigogi guda biyu da ƴan ta’addan suka watsar.

Bugu da ƙari, mayaƙan na ISWAP sun sanya wani bam da nufin mamayar dakarun sojojin.

Jami'an tsaro sun lalata bam ɗin ƴan ta'adda

Sai dai, jami’an tsaro sun yi nasarar lalata bam ɗin cikin kwarewa, wanda hakan ya hana sanya bai haifar da wata illa ba.

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

Wannan nasarar da sojojin suka samu ya nuna irin jajircewa da sadaukarwar da suke yi don tabbatar da tsaro a yankin.

Sun kuma tabbatar da cewa ba za su bari ƴan ta’adda su samu damar cutar da rayukan al’umma ko lalata dukiyoyin jama'a ba.

Gwamnati da hukumomin tsaro dai sun sha yin kira ga mazauna yankin su ci gaba da ba da goyon baya ga jami’an tsaro ta hanyar kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Ƴan ta'addan a yayin harin sun ƙona motocin jami'an rundunar CJTF da sojoji bayan sun shigo ƙauyen da safe.

Dakarun sojoji sun nuna bajinta inda suka fatattaki ƴan ta'addan bayan an ɗauki dogon lokaci ana ƙazamin artabu a tsakanin ɓangarorin guda biyu.

Kara karanta wannan

Ana jiran kashe Bello Turji, sojoji sun sheke hatsabibin kwamandan 'yan ta'adda

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng