Bayan Hukuncin Kotu, Gwamna Uba Sani Ya Maida Sarkin da El Rufai Ya Tuge kan Sarauta
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya mayar da Jonathan Paragua Zamuna a matsayin sarkin Piriga bayan sauke da shi da gwamnatin da ta gabata ta yi
- Gwamna Sani ya bayyana jajircewarsa wajen mutunta doka da adalci, tare da yin kira ga sabon sarkin ya mulki kowa ba tare da bambanci ba
- Cikin farin ciki, Sarkin Zamuna ya gode wa Gwamna bisa dawowa mulkinsa, yana mai yabawa da ci gaban gwamnatin a bangarorin ilimi da lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya dawo da Jonathan Paragua Zamuna matsayin Sarkin Piriga a Karamar Hukumar Lere, bayan kotu ta wanke shi.
Hakan ya biyo bayan hukuncin Kotun Kwadago ta Kaduna da ta soke tsige Sarki Zamuna a ranar 14 ga Yunin 2024.

Source: Twitter
El-Rufai ya tsige Sarki kwanaki kafin barin mulki
Gwamna Uba Sani ya tabbatar wannan labari ne a yammacin yau Laraba 22 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan tsige Sarkin da magabacinsa, Nasir El-Rufai, ya yi a ranar 22 ga Mayun 2023, kwanaki kafin karewar wa’adinsa na mulki.
Tsohon gwamnan Kaduna ya tunbuke Sarakuna biyu da Hakimai uku daga kan karagar mulki bisa kama su da aikata laifuka.
Malam Nasiru El-Rufai ya umarci Masarautun Piriga da Arak su fara shirin bin matakan da ya dace domin naɗa sabbin Sarakuna.
Gwamna Uba Sani ya mayar da basarake a Kaduna
A wajen bikin dawo da sarkin a dakin taro na Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna, Gwamna Sani ya taya Sarkin Zamuna murna, yana mai jaddada mulki ba tare da wariya ba.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa na aiki bisa bin doka da adalci, yana mai ce zai tabbatar da gaskiya a lamarin.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
“Muna jajircewa kan gaskiya da adalci a dukkan ayyukanmu.”
“Wannan lokaci ne na tunani ga gwamnati da al’umma, mu duba ko ayyukanmu na kawo zaman lafiya ko rarrabuwar kai.”
- Uba Sani
Ya yi kira ga Sarkin da aka mayar ya ja ragamar mulkinsa cikin sadaukarwa da tausayi.
Gwamna Sani ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaban jihar, tare da alkawarin zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar Kaduna.
Basarake ya gode wa gwamna Uba Sani
Cikin farin ciki, Sarkin Zamuna ya gode wa Gwamna Sani bisa dawowa mulkinsa, yana mai cewa gwamnan rahama ne ga jihar Kaduna.
“Jagorancinku ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jiharmu, Kun nuna adalci da gaskiya, kuma muna gode muku."
- Cewar basaraken
Sarkin ya kuma yaba da kokarin gwamnatin kan ci gaban al’umma a bangaren zuba jari a ilimi, kiwon lafiya, da ababen more rayuwa.
Uba Sani ya yaba wa manufofin Tinubu
A baya, kun ji cewa Gwamnan jihar Kaduna ya nuna gamsuwarsa kan manufofin gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Uba Sani ya bayyana cewa manufofin na Tinubu na da nufin sake fasalin ƙasar nan ta yadda za ta samu ci gaba mai ɗorewa.
Ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara sanya juriya domin a cewarsa nan ba da daɗewa za a fara ganin amfanin manufofin na Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

