'Qur'anic Festival': Malamin Musulunci Ya Kalubalanci Dan Bello, Ya Fadi Matsayarsa
- Sheikh Adam Muhammad (Albaniy Gombe) ya yi kira ga al’umma su rika yin adalci a duk wani batu da ya shafi addini ko siyasa
- Malamin ya bayyana cewa addu’o’in kawar da azzaluman shugabanni na da amfani, amma kada a rika sanya siyasa a cikin lamarin
- Shehin ya ce duba da bayanan Bala Lau, Dan Bello, da Ahmad Sulaiman, mutane su rika tantance gaskiya kafin yarda da labarai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gombe - Sheikh Adam Muhammad watau Albaniy Gombe ya yi karin haske kan ce-ce-ku-ce da ake yi game da 'Qur'anic Festival'.
Shehin malamin ya ce ya kamata al'umma su rika adalci a dukan wata magana da aka gabatar a kafofin sadarwa.

Asali: Facebook
Albaniy Gombe ya bukaci addu'a ga azzaluman shugabanni
Sheikh Albaniy ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba 22 ga watan Janairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya ce ya saurari dukan bayanai daga Bala Lau da wani mai sarauta a Katsina fa Dan Bello da kuma Ahmad Sulaiman kan lamarin.
Ya ce babu matsala idan har addu'a za a yi Allah ya kawar da azzaluman shugabanni da ke cutar da al'umma.
"Idan abu ne aka shirya domin goyon bayan wasu a siyasa mu ba mu cikinsa amma bayanai da na samu musamman daga Bala Lau da Dan Bello da wasu, na fahimci wannan abin ba yau aka fara ba."
"Magana ce jimammiya saboda Ahmad Sulaiman ya ce tun lokacin mulkin Buhari, kai tun ma kafinsa aka fara wannan magana."
"Duba da wadannan bayanai, don Allah idan za a karanta Alkur'ani duk mugun da ke kasar nan Ubangiji ya kawar mana bai kamata a yi ba?"
- Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe
Matsayar Albaniy Gombe kan Qur'anic Festival
'Ni a matsayi na idan har an addu'a ce domin rokawa ƙasar nan alheri ai ba matsala, mutane dubu 30 wasa ne."

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
"Bala Lau dubu 30 ya ce shi wancan kuma dubu 60, ka ga a nan bai san abin da ke faruwa ba, amma a yau a kafafen sadarwa babu wanda ake gaskatawa kamarsa."
- Sheikh Adam Muhammad Albaniy
Malamin ya koka kan yadda al'umma ke yarda da abin da bai zo ya faru ba inda ya ce shi Ɗan Bellon ya san gaibu ne.
Ya ce ko Dan Bello ya yi alkawari da Allah cewa abin da ya fada dole zai faru? da har mutane suka gamsu da maganganunsa.
Izalah ta yi magana kan 'Qur'anic Festival'
Kun ji cewa Sheikh Ibrahim Idris ya yi karin haske kan zargin da ake yi cewa za a yi amfani da taron Qur'anic Festival domin tallata Bola Tinubu a 2027.
Malamin ya bayyana cewa taron ba na Izala ba ne, Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA) ce ke shirya shi.
Ya yi gargadi ga masu siyasantar da taron tare da tabbatar da cewa manufarsa ita ce inganta koyarwa da haddar Alkur’ani mai girma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng