Jarrabawa Ta Sake Faɗawa Mutane, Tanka Maƙare da Fetur Ta Kama da Wuta a Kusa da Gidaje
- Wata tanka maƙare da man fetur ta yi bindiga tare da kamawa da wuta a Ibadan, ta kashe direba tare da jikkata yaron motar
- An ruwaito cewa tankar ta ci karo da wasu manyan motoci bayan ta kufce wa direban, sannan ta faɗa wani rami da ke kusa da babban titin Ojoo zuwa Iwo
- Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta bayyana cewa jami'anta sun yi nasarar kashe wutar da ta kama bayan faɗuwar tankar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Wata tanka dauke da man fetur ta yi bindiga a tsakiyar gidajen mutane, ta kashe direbanta tare da jikkata wani mutum guda a Ibadan.
Babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Mista Yemi Akinyinka, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Oyo.

Asali: Original
Tankar mai ta kama da wuta a Ibadan
Ya bayyana cewa tankar ta kucce wa direban, ta yi karo da wasu manyan motoci guda biyu, sannan ta kife a wani rami da ke kusa da titin ta kama da wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Akinyinka ya ce hatsarin ya yi sanadiyyar mutuwar direban tankar yayin da aka ceto yaron motar da ransa duk da ya jikkata, Vanguard ta tattaro.
“Wannan mummunan lamarin mara daɗi ya faru ne a kusa da gidan Fijabi da ke Agbowo, kan babban titin Ojoo zuwa Iwo a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
“Mun samu kiran gaggawa kan gobarar da ta kama bayan faɗuwar tankar da misalin ƙarfe 2:45 na safe ta wayar tarho.
“Mun hanzarta tura ma’aikata zuwa wurin, inda suka dakile yaduwar gobarar zuwa gidajen mutane da ke kusa.”
- Yemi Akinyinka.
Faɗuwar tankar ya shafi wasu motoci 3
Shugaban hukumar kwana-kwana ta Oyo ya ƙara da cewa da zuwan jami'an kashe gobara, sun tarar da motoci sun kama da wuta a wurin, rahoton Tribune.
“Da muka isa wurin, mun tarar da manyan motoci uku suna ci da wuta, kowace mota tana da nisan mitoci 20 tsakaninta da wata."
“Direban tankar ya kone kurmus yayin da muka yi nasarar ceto yaron motar a raye, kuma yanzu haka an kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan (UCH) domin kula da lafiyarsa," in ji shi.
Ibadan: Tankar ta ƙone a hatsarin
Akinyinka ya bayyana cewa tankar ta lalace gaba ɗaya sakamakon gobarar, amma an samu damar ceto sauran manyan motocin guda biyu daga lalacewa.
Ya ce shugaban sashen ayyuka na hukumar kashe gobara Mista Ismail Adeleke, tare da tawagarsa, ‘yan sanda, da sauran jami’an tsaro, sun kasance a wurin domin tabbatar da tsaro da hana tashin hankalin jama’a.
Gobara ta babbake kayan miliyoyi a Ibadan
A wani labarin, kun ji cewa ƴan kasuwa sun tafka asara da wata mummunar gobara ta tashi da tsaɗkar dare a kasuwar sayar da kayan gyara a Ibadan.
Gobarar wanda ta fara ci da karfe 2:00 na tsakar dare ta yaɗu zuwa shagunan ƴan kasuwa duk da ƙoƙarin jami'an kwana-kwana na kashe ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng