Ma'aikata Sun ga Ta Kansu, Gwamna a Arewa Ya Kai Ziyarar Bazata, Ya Yi Barazanar Kora
- Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya kai ziyarar bazata sakatariyar jihar inda ya gano yadda ma'aikata ke wasa da aikinsu
- Mai girma Rabaren Hyacinth ya kulle daruruwan ma’aikata yayin ziyarar a sakatariyar, inda ya samu ma’aikata ‘yan kadan
- Ya nuna takaicinsa kan halin ma’aikata yayin da yake ziyartar ma’aikatu, yana mai bayyana damuwa kan rashin aiki da gaskiya
- Alia ya gargadi ma’aikata cewa yana da iko da hanyar sallamar su, yana masu jan hankali kan hadarin da ke tattare da rashin biyayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makurdi, Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya yi wa ma'aikatan jihar bazata a yau Laraba 22 ga watan Janairun 2024.
Gwamna Hyacinth ya kulle daruruwan ma’aikata yayin ziyarar bazata a sakatariyar jihar, da ya samu ma’aikatan da suka zo ba su da yawa.

Asali: Twitter
Gwamna Alia ya kara albashin ma'aikata
Punch ta ce Gwamnan ya isa wurin ziyarar kimanin karfe 10:35 na safe domin duba aikin gyaran sakatariyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Gwamnatin Benue ta sanar da ƙarin albashin ma'aikata zuwa N75,000 bayan wani zama da ta yi da kungiyar kwadago a fadin jihar.
Gwamna Hyacinth Aliya ya bayyana dalilin zarce N70,000 da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Haka zalika gwamna Alia ya yi alkawarin cigaba da yin ayyukan da za su saka ma'aikatan jihar Benue walwala da sauƙin rayuwa.
Gwamna ya kai ziyarar bazata ga ma'aikata
Yayin da yake zagayawa cikin ma’aikatu, gwamnan ya nuna takaicinsa kan rashin zuwan wasu kwamishinoni da manyan jami’ai wajen aiki.
Lokacin da yake shirin barin sakatariyar, gwamnan ya yi jawabi ga ma’aikata da suka taru a bakin kofa, yana sukar halin ko-in-kula wajen aiki.
“Abin da kuke yi yana haifar wa iyalanku matsala, ba za ku samu ci gaba ba saboda cin amana da rashin gaskiya wajen aiki.”

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
“Ayyukan da nake yi ba don kai na ba ne, sai don mutanen da ba su san ni ba ko wadanda ba su gani na ba.”
- Alia Hyacinth
Gwamna Alia ya gargadi ma'aikatan Benue
Gwamnan ya gargadi ma’aikata cewa yana da hanyar samun sunayensu da kuma sallamarsu, yana masu jan hankali kan hadarin rashin da’a.
Ya kuma yi barazanar korar ma'aikata inda ya caccaki kwamishinoni da dama da ba su fito aiki a kan lokaci ba a jihar
“Ku yi abin da ya dace, idan ba don kanku ba, sai don mutanen da kuke kulawa da su domin su ke shan wahala.”
- Alia Hyacinth
Gwamna Hyacinth ya gargadi yan bindiga
Kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya ɗauki zafi kan harin da aka kashe mutane 11 a kauyen Anwase a ƙaramar hukumar Kwande.
Alia ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa masu hannu a mummunan harin sun fukanci fushin doka.

Kara karanta wannan
'Ni kadai ke da iko': Gwamnan APC ya rikita zaman makoki, ya gargadi maciya amana
Gwamnan ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan da suka rasa ƴan uwansu tare da fatan samun lafiya ga waɗanda suka jikkata a harin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng