"Bai Dace ba:" Jafar Jafar Ya Soki Yadda Gwamna Abba Ya Buge da Raba Awaki a Kano
- Fitaccen dan jarida, Jafar Jafar ya bayyana rashin jin daɗinsa kan tsarin raba awaki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi
- Gwamnan jihar Kano ya raba awaki akalla sama da 7,000 ga mata a Kano domin ba su damar yin kiwo domin magance talauci
- Jafar ya yi kira da a mayar da hankali kan ayyuka na zamani, yana mai nuna cewa rabon dabbobi a karni na 21 bai dace da tsarin mulki ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Fitaccen dan jaridar nan, Jafar Jafar ya bayyana rashin gamsuwa da tsarin da gwamnatin Kano ta bi wajen raba awaki ga matan karkara a ranar Talata.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, da kansa ba sako ba ya rika mikawa matan karkara awaki da yawansu ya kai kimanin 7,158 ga mata 2,383 a Mariri, karamar hukumar Kumbotso.

Source: Facebook
A sakon da Jafar Jafar ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce abin zai zama son kai matukar bai yi magana a kan sigar da gwamnati ta yi rabon ba.
Ya ce an san yadda su ka rika sukar irin wannan rabo a kan wasu 'yan siyasa da su ka fito daga jam'iyyar PDP a baya, kuma lamarin bai dace da gwamna ba.
Isa Ashiru ya shahara da batun awaki lokacin da yake neman doke Uba Sani a zaben Kaduna, a dalilin haka aka ji mutane suna sukar wannan tsari a 2023.
Jafar Jafar bai ga laifin rabon dabbobi ba
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa dan Jafar Jafar na ganin irin wannan aiki, abu ne da ya dace da shugabannin kananan hukumomi.
Ya kara da cewa musamman a yanzu da kotu ta mikawa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu, bai dace a ga gwamna ya na yin aikin da ya dace su yi ba.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Dan jaridar ya ce;
“Yanzu da ƙananan hukumomi suka samu ‘yancin cin gashin kai, kamata ya yi a bar musu rabon jarin dabbobi da wilbaro.
“Ya zama dole mu gaya wa Gwamnan gaskiya saboda mun tallata wa mutane shi da tunanin cewa daban yake da saura,” in ji Jaafar Jaafar.
"A karni na 21 muke," Jafar Jafar
Fitaccen dan jarida ya ce ya kamata Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuna cewa a karni na 21 ake, lokacin da fasaha ta ƙirƙirarriyar basira AI, motoci da jirage marasa matuƙa ke tashe.
“Da farko dai akwai abubuwan da bai kamata a ga Gwamna a ciki ba. Daukar mataki guda ɗaya da zai iya tada ƙura ka iya lulluɓe duk wasu matakai masu kyau na kawo ci gaba da dan siyasa ya yi a mulkinsa. Kuma da wancan ɗayan za a ci gaba da tuna shi ko ba ya nan.
“Misali, mun fi tuna tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan barnatar da $16bn (bayan $3.55 ne) a harkar gyaran wutar lantarki fiye da gina tashoshin wutar lantarki 10 da ya yi karƙashin shirin NIPP.

Kara karanta wannan
'Annabi ya fadi amfanin namansu ga lafiya': Abba Kabir ya kare matakin raba awaki a Kano
“Kano kullum na yabon Legas saboda tsare-tsare da shirye-shiryen da ta gina kanta da su, amma idan jagororinmu suka zo da wasu shirye-shiryen sai ka zaci mutanen zamanin da suke mulka.
Gwamna ya raba awaki
A baya, mun ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba awaki sama da 7,000 a Mariri da ke karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano domin rage talauci a tsakanin mata.
Rabon shi ne zagaye na biyu da gwamnatin Kano ta fara, inda gwamnatin ta ce za a cigaba da rabon awaki da tumaki ga matan karkara a wani yunkuri da yaki da talauci.
Asali: Legit.ng
