Yan Sanda Sun Yi Ram da Dalibar da Ta Yi Yunkurin a Fille Kan Malaminta a Kano
- 'Yan sanda a Kano sun cafke wani saurayi da budurwarsa bisa zargin kai hari kan wani malami a Kwalejin Fasaha ta Kano
- Khadija Hassan, ta yi zargin cewa malamin ya zama cikas ga burin karatunta, wanda ya jawo rikici har aka kai masa hari
- Matakin da ɗalibai da ma’aikatan makaranta su ka dauka na shiga tsakani ne ya hana lamarin rikidewa zuwa kisan kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - 'Yan sanda a Kano sun kama wasu ɗalibai bisa zargin kai hari kan wani malami a kwalejin Fasaha ta jihar Kano a makon da ya gabata.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an tsare saurayin ɗalibar, Khalid Hussain, mai shekaru 20 da Khadija Hassan, mai shekaru 18.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa saurayin dan unguwar Dorayi ne, ita kuma Khadija ta fito daga unguwar Charanchi, kuma dukkaninsu su na tsare a sashen Anti-Daba na rundunar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin da aka kai wa harin, Aliyu Hamza Abdullahi, ya shigar da ƙorafi ga 'yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike don tabbatar da cewa an hukunta wanda ake zargi da laifin.
Yadda ɗalibai suka kai wa malami hari
Rahotanni sun nuna cewa ɗalibar ce tare da saurayinta ne su ka kitsa harin har Khadija ta gayyaci Khalid zuwa ofishin malamin da ke kwalejin fasaha ta Kano.
Khadija ta yi zargin cewa malamin ya zama cikas ga burin da ta ke da shi a makarantar, saboda haka ta yi yunkurin daukar hukunci a hannunta.
Musabbabin kai wa malami hari a Kano
Cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, Auwal Isma’ila Bagwai ya fitar, ya ce ɗalibar tana son canji zuwa wani sashe daban na karatu.

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
Sai dai malamin da ke kula da wannan, Aliyu Hamza Abdullahi ya shaida mata cewa ba ta cika ƙa’idojin darussa da ake buƙata ba.
Saboda haka, cikin fushi, ɗalibar ta dora laifin kan malamin tare da kiran saurayinta don ya hukunta shi.
Kano: Yadda dalibai su ka ceci malaminsu
Rahotanni sun bayyana cewa Malam Aliyu ya tsira da kyar bayan Khalid ya nufe shi da zaftareriyar wuka domin cire masa kai.
Sai dai daliban da ke zaune a wurin sun yi saurin daukar mataki tare da shiga tsakani, wanda hakan ya takaita illar da Khalid ya yi wa malamin.
'Yan daba sun hana kama dalibar Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan daba sun takawa jami'an tsaron kwalejin fasaha ta Kano birki a yunkurin da su ke yi na cafke ta bisa zargin ta kai hari ga malamin makarantar.
Ta kai harin ne bisa zargin da ta ke yi na cewa Malam Aliyu Hamza Abdullahi ya hana ta rawar gaban hantsi, bayan ta ki amincewa ta sauya kwas din da ta ke karanta zuwa wanda ta ke so.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng