Gwamna Uba Sani Ya Yabi Manufofin Shugaba Tinubu, Ya Fadi Abin da Za Su Yi

Gwamna Uba Sani Ya Yabi Manufofin Shugaba Tinubu, Ya Fadi Abin da Za Su Yi

  • Gwamnan jihar Kaduna ya nuna gamsuwarsa kan manufofin gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Uba Sani ya bayyana cewa manufofin na Tinubu na da nufin sake fasalin ƙasar nan ta yadda za ta samu ci gaba mai ɗorewa
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara sanya juriya domin a cewarsa nan ba da daɗewa za a fara ganin amfanin manufofin na Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi maganan kan manufofin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa shugaba Tinubu ya ƙudiri aniyar sake fasalin Najeriya tare da tabbatar da ɗorata a kan turbar ci gaba mai ɗorewa.

Uba Sani ya yabi Tinubu
Gwamna Uba Sani ya ce manufofin gwamnatin Tinubu za su sauya Najeriya
Source: Twitter

Tashar Channels tv ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin wani taron tattaunawa na rana ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank ta shirya a ranar Talata, 21 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya faɗi amfanin manufofin Tinubu

Uba Sani ya bayyana cewa da an ɗan ƙara jurewa, za a fara cin gajiyar sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya kawo, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Gwamnan ya amince cewa aiwatar da manufofin shugaban ƙasan sun zo da irin nasu ƙalubale da raɗaɗi ga ƴan Najeriya ba, amma ya bayyana cewa wahalar ta ɗan lokaci ce.

“A zahiri, mun fara ganin haske. Tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa. Ba da daɗewa ba za a fara ganin tasirin manufofin gyaran da aka aiwatar a Najeriya. Abin da shugaban ƙasa ke buƙata a wannan lokacin shi ne goyon bayan al’ummarmu."
A cewar gwamnan, domin sake fasalin Najeriya da ba ƴan Najeriya madafa, dole ne a mayar da hankali kan noma.
"A lokacin samun ƴancin kai, noma shi ne ginshiƙin tattalin arziƙin Najeriya. Yankuna guda uku na wancan lokacin sun yi amfani da albarkatun da aka samo daga noma wajen gina muhimman ababen more rayuwa."

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

"Saboda gano man fetur, sai muka yi watsi da noma. Mun shiga mawuyacin hali saboda hakan. Dole ne mu koma noma kuma mu zuba jari mai yawa a cikin harkar. Shi ne mabuɗin warware matsalolin talauci, rashin aikin yi da rashin tsaro."
"Shugaba Bola Tinubu ya riga ya fara nuna mana hanya. Gwamnatinsa ta fifita noma kuma tana zuba jari sosai a cikinsa da kuma ƙarfafa ƙananan manoma."
“Shugaban ƙasa yana kuma bayar da tallafi mai ɗorewa ga jihohi dangane da kuɗaɗe da kayan aikin gona.”

- Gwamna Uba Sani

A cewar Gwamna Uba Sani, zuba jarin da Tinubu ya yi a harkar noma, bai yi kama da na kowace gwamnati a tarihin Najeriya ba.

Shugaba Tinubu ya kafa makarantar kimiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar makantar kimiyya da fasaha a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasa bola Ahmed ya raɗawa sabuwar makarantar wacce za a samar a Gwarinpa, sunansa domin ya karrama kansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng