Gwamnan Neja Ya Ji Tausayin Talakawa, Zai Rabawa Matasa da Manoma Tallafi a Intanet?

Gwamnan Neja Ya Ji Tausayin Talakawa, Zai Rabawa Matasa da Manoma Tallafi a Intanet?

  • Gwamnatin jihar Neja ta fito ta karyata rahotannin da ke cewa ta shirya rabawa matasa da manoma tallafi ta yanar gizo
  • Sakataren gwamnati, Abubakar Usman ya ce 'yan damfara ne ke son amfani da kokarin gwamnati wajen damfarar mutane
  • Abubakar Usman ya fadawa matasa, da ma al'ummar jihar hanyoyin da za su rika samun sahihina shirye-shiryen gwamnati

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Gwamnatin jihar Neja ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta bude shafin rijistar ba da tallafi ga matasa da manoma.

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Usman, ya bayyana labarin a matsayin na damfara, inda ya ce an yi ne don karkatar da kokarin Gwamna Mohammed Bago.

Gwamnatin Neja ta karyata rahotannin da ke yawo na cewa ta na shirin ba matasa da manoma tallafi
Gwamnatin Neja ta ce ba ita ce ta bude shafin da ke ikirarin ba matasa da manoma tallafi ba. Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Gwamnatin Neja ta karyata rahoton ba da tallafi

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Abubakar Usman ya gargadi 'yan jihar da su yi hattara da shiga wannan shafin na 'yan damfara, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Sanarwar ta ce:

“Gwamnatin jihar Neja ta samu labarin wani shafin yanar gizo na damfara da ke ikirarin cewa gwamnati ce ta bude domin matasa da manoma su yi rijistar samun tallafi."

Ya kara da cewa gwamnatin ba ta kaddamar da wani shafi makamancin wannan ba, kuma ya gargadi jama’a da su rika nisantar duk wani abu mai kama da damfara.

Gwamnati ta fadi hanyar isar da sako a Neja

Abubakar Usman ya ce za a rika sanar da duk wani shiri na gwamnati ta shafukan gwamnati a hukumance ko kuma shafukan sada zumunta da aka amince da su.

“Za a bayyana duk wani shirin tallafi da aka kaddamar ta wadannan kafafen gwamnati na da aka amince da su a hukumance,” inji Usman.

Ya yi kira ga jama’a da su guji bayar da bayanan sirrinsu a irin wadannan kafafen damfara, tare da kasancewa masu lura da tsaro.

Kara karanta wannan

Jigawa: Gwamna zai ciyar da mabukata 189, 000 a Ramadan, an ji kudin da zai kashe

Neja: Gwamnati ta gargadi matasa da manoma

Sakataren ya yi gargadin cewa irin wadannan kafafen suna amfani da sunan gwamnati don yaudarar jama’a da karbar bayanansu.

Abubakar Usman ya jaddada cewa akwai bukatar jama’a su kasance masu kula, kuma su tabbatar da bin sahihan kafafen gwamnati don samun bayanai.

Ya kuma bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani abu mai kama da damfara ga hukumomin tsaro don daukar mataki na gaggawa.

Gwamnan Neja ya fara biyan sabon albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, NLC reshen Neja ta yaba wa Gwamna Muhammad Umaru Bago kan fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.

Shugaban NLC NA JIHAR, Idris Lafene, ya ce aiwatar da sabon albashin a watan Nuwamba 2024 ya rage wahalhalun tattalin arziki ga ma’aikata.

Lafene ya tuno yadda Gwamna Bago ya bayar da umarni a tabbatar an aiwatar da sabon albashin kafin ya bar jihar, wanda ya faranta wa ma’aikatan rai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com