Dama Ta Samu: Gwamnatin Tinubu Za Ta Dauki Matasa Aiki a Dukkanin Jihohin Najeriya

Dama Ta Samu: Gwamnatin Tinubu Za Ta Dauki Matasa Aiki a Dukkanin Jihohin Najeriya

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta bude shafin daukar matasa aiki a karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP daga dukkanin jihohin Najeriya
  • Gwamnatin ta sanar da cewa za ta ba wadanda aka dauka aikin alawus mai gwabi da kayan aiki don kawo sauyi a tsarin kiwon lafiya
  • Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla yadda matasa 'yan kasa da shekaru 35 za su iya neman wannan aikin da takardun da ake bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bukaci 'yan Najeriya masu sha’awar aikin kiwon lafiya da su nemi shiga shirin 'Masu Kula da Lafiya na Kasa'.

Bayo Onanuga, mai taimaka wa Shugaba Tinubu a fannin yaɗa labarai, ya bayyana cewa za a dauki matasa 'yan kasa da shekaru 35 ne aiki a karkashin shirin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Bayo Onanuga ya yi bayani game da daukar aikin da gwamnati za ta yi a shirin kiwon lafiya
Gwamnatin Bola Tinubu za ta dauki matasa aiki a karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP. Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

NHFP: Gwamnati za ta dauki matasa aiki

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Onanuga ya ce za a tura waɗanda aka dauka aikin zuwa ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta tabbatar cewa waɗanda aka zaɓa za su samu alawus mai gwabi da kayan aiki domin su kawo gagarumin sauyi a bangaren kiwon lafiya a Najeriya.

Onanuga ya bayyana cewa za a rufe neman aikin a ranar Litinin, 27 ga Janairun 2025.

Ya kuma ce za a iya samun karin bayani a nan: https://healthfellows.ng/apply

Abin da sanarwar Onanuga ta ce

Sanarwar Bayo Onanuga ta kara da cewa:

“An buɗe shafin neman aiki a shirin matasa 'Masu Kula da Lafiya a Najeriya':
“Gwamnatin Tinubu na kira ga matasa 'yan Najeriya da su shiga shirin matasa Masu Kula da Lafiya.
“Matasan da za a zaɓa, daga shekara 25 zuwa 35, za su yi aiki a dukkanin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

“Za su sami alawus da kayan aiki na zamani domin kawo cigaba a tsarin kiwon lafiya.”

Yadda matasa za su nemi aikin NHFP

A shafin yanar gizon shirin NHFP, masu neman aikin za su cike fom sannan su tabbatar sun cike dukkanin ka'idoji, in ba haka ba, ba za a ɗauke su aikin ba.

Ana kuma shawartar masu neman aikin su tanadi waɗannan takardun domin gabatarwa lokacin tantancewa idan sun tsallake matakin farko:

  • Takardar haihuwa ko rantsuwar ɗage shekara
  • Takardar CV
  • Shaidar digiri daga jami'a
  • Takardar shaidar jihar mutum ta asali
  • Shaidar kammala NYSC

Gwamnati ta gargadi masu nema da cewa duk wata ƙarya ko karya doka da suka yi yayin neman aikin zai haifar da ƙin amincewa da bukatarsu.

2024: Tinubu ya gabatar da shirin tallafi 11

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya na da damar neman akalla tallafi 11 da gwamnatin tarayya ta samar don sauƙaƙawa al'ummar ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya za ta dauki ƴan Najeriya aiki, an lissafo abubuwan da ake bukata

Waɗannan shirye-shiryen sun haɗa da fannoni kamar ilimi, sufuri, kasuwanci, gidaje, da sana'o'in dogaro da kai.

Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin sadarwar zamani, Olusegun Dada, ya bayyana waɗannan shirye-shirye tare da shafukansu na yanar gizo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel