An Dakatar da Malamin Addini daga Yin Wa'azi a Najeriya Saboda Ya Auri Baturiya

An Dakatar da Malamin Addini daga Yin Wa'azi a Najeriya Saboda Ya Auri Baturiya

  • Cocin Katolika ta Warri ta dakatar da RabaranOghenerukevwe daga aikin limanci saboda auren sa da Ms. Dora Chichah a Amurka
  • Sanarwar ta bayyana cewa Oghenerukevwe ya samu dakatarwa ta Latae Sententiae bisa karya dokokin coci, kuma ba zai yi wa'azi ba
  • Cocin ta roki Ubangiji ya ba Oghenerukevwe damar yin tunani a kan kuskuren da ya yi, da ba shi mafita kan matsalar da jefa kansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Cocin Katolika ta Warri ta dakatar da Rev. Fr. Daniel Okanatotor Oghenerukevwe daga aikin limanci bayan an samu rahoton aurensa a Amurka.

An fitar da bayanin hakan a cikin wata sanarwa mai taken: 'Sanarwar Dakatarwa', a ranar Alhamis, 16 ga Janairun 2025, tare da sa hannun Bishop na Warri.

Cocin Katolika ta Warri ta yi magana da ta dakatar da wani babban fasto dinta
Cocin Katolika a Warri ta dakatar da babban fasto saboda ya auri 'yar Amurka.
Asali: Getty Images

Coci ta dakatar da babban fasto

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Sanarwar ta ce Oghenerukevwe ya yi aure da Ms. Dora Chichah a Cocin Streams of Joy a Dallas, Amurka, ranar 29 ga Disambar 2024, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta kara da cewa bidiyon aurensa da baturiyar ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, wanda ya jawo hankalin jama'a.

Bisa ga wannan lamari, cocin Katolika ta ce ta dakatar d Rabaran Oghenerukevwe, dakatarwa mai tsanani ta Latae Sententiae bisa karya dokokin cocin.

Abin da ya faru kafin dakatar da faston

Sanarwar cocin ta ce:

"Rabaran Anthony Ovayero Ewherido, shugaban fastoci na Katolikar Warri, ya tabbatar da cewa an dakatar da Rabaran Oghenerukevwe daga gudanar da aikin limanci."

Rabaran Ewherido ya shaida cewa Rabaran Oghenerukevwe ya tuntube shi a ranar 30 ga Nuwambar 2024, daga kasar Amurka.

"Ya nemi a sake duba nauyin da aka dora masa, ya kuma bukaci a sallame shi daga dukkanin alhakin limanci a cikin Cocin ta Katolika."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

- A cewar sanarwar.

Aure da baturiya ya jawo aka dakatar da faston

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Amma a ranar 29 ga Disamba, 2024, Rabaran Oghenerukevwe ya yi aure da Ms. Dora Chichah a Cocin Streams of Joy a Dallas.
"Bayan wannan aika-aikatar, an yi amfani da dokar Latae Sententiae bisa dokokin Canon 1394 §1 wajen dakatar da Rev. Fr. Daniel Oghenerukevwe daga limanci.
"A domin haka, an hana shi gabatar da kansa a matsayin limamin Cocin Katolika ta Warri, kuma yana da hakkin jayayya da hukuncin karkashin Canon 1734 §1."

"Muna rokon Ubangiji ya ba shi damar yin tunani a kan wannan kuskure da ya yi, ya kuma ba shi mafita cikin sauki kan abin da zai fuskanta"

Cocin RCCG ta dakatar da wasu fastoci 2

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Cocin RCCG ta dakatar da wasu fastoci biyu bisa zarginsu da aikata babban laifi da ya saɓawa koyarwar Littafi Mai Tsarki.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

Fasto Ayorinde Ade Bello da Deacon Oke Mayowa suna fuskantar zargin aikata luwadi, wanda Cocin RCCG ta bayyana matsayin laifi mai tsanani da ya saɓa Injila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.