NAFDAC Ta Garkame Wani Babban Kantin Sayar da Magunguna a Abuja, Ta Fadi Dalili
- NAFDAC ta rufe kantin magani a Abuja saboda sayar da magunguna da suka lalace, bayan rahoto daga wani mai kwarmato
- Tawagar binciken NAFDAC ta gano kayayyakin da suka lalace na sama da N7m, ciki har da kayan gwaji da ke barazana ga lafiya
- An cafke shugaba da magatakarda na kantin domin bincike, tare da tabbatar da hukunci mai tsauri don dakile irin wannan dabi’a
- Amfani da magungunan da suka lalace na haifar da illa ga lafiya da kuma nakasa tsarin garkuwar jiki, inji Dakta Shamsuddeen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar NAFDAC ta rufe wani kantin magani da ke Onitsha Crescent, Area 11 – Garki, Abuja, saboda sayar da magunguna da suka lalace kuma ba su da rijista.
Wannan mataki ya biyo bayan rahoto daga wani mai kishin kasa, wanda ya sa hukumar ta gudanar da bincike.

Asali: Twitter
Abuja: NAFDAC ta rufe kantin magunguna
Hukumar NAFDAC ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X (tsohuwar Twitter) a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin binciken, NAFDAC ta gano magunguna da suka lalace wanda darajarsu ta kai sama da Naira miliyan bakwai, ciki har da "H-Pylori" na kayan gwaje gwaje.
Wannan kayan gwaji na da hadari sosai ga lafiyar jama’a, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Abin da NAFDAC ta ce a Abuja
Hukumar ta cafke babban darakta da babban magatakarda na kantin don gudanar da karin bincike kan al’amarin.
Sanarwar ta ce:
"NAFDAC ta rufe kantin magani a Onitsha Crescent, Area 11 – Garki, Abuja, kan sayar da magunguna da suka lalace kuma ba su da rijista."
"Tawagar bincike ta gano kayayyaki da suka lalace, wadanda darajarsu ta kai sama da naira miliyan bakwai, ciki har da kayan gwaji masu hadari ga lafiyar jama’a."
NAFDAC ta nemi hadin kan jama'a
Duk da kokarin ma’aikatan kantin maganin na hana binciken, tawagar ta samu nasarar kwace kayan da suka lalace kuma ta kulle wurin.
An cafke shugaba da wani jami'in kantin domin amsa tambayoyi, tare da tabbatar da sanya tsauraran hukunci don kawo karshen irin wannan dabi’a.
NAFDAC ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura yayin sayen kayayyakin da ake sarrafawa tare da kai rahoton duk wani abu da ake zargi ofishin hukumar mafi kusa.
Illolin shan magungunan da suka lalace
Da muka tuntubi Dakta Shamsuddeen Abubakar, ya shaida mana cewa akwai hadari sosai a shan magungunan da suka lalace.
Dakta Shamsuddeen ya ce amfani da magungunan da suka lalace yana iya haifar da mummunar illa ga lafiyar dan Adam, yana mai cewa:
"Magungunan da wa'adin amfani da su ya kare sun da illa domin za su iya haifar da rashin lafiya mai tsanani ga mutum."
Magungunan da suka lalace suna dauke da sinadarai da za su iya zama masu cutarwa ga garkuwar jiki, a cewar likitan, inda ya kara da cewa:
"Magungunan da suka lalace na iya zama tushen yaduwar cututtuka, musamman ma ta hanyar nakasa tsarin garkuwar jiki."
NAFDAC ta rufe kamfanoni a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an NAFDAC a Kano sun kai sumame wasu kamfanonin yin magungunan dabobi a Bichi, jihar Kano.
NAFDAC ta kama masu kamfanonin magungunan kan zargin yin magunguna marasa inganci da sayar da su da lambar NAFDAC ta bogi.
Hukumar ta ce ta shafe watanni shida tana bincike kan magungunan kamfanonin, bayan lura da karuwar magungunan jabu a kasuwannin Kano.
Asali: Legit.ng