Jami'an Tsaro Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Aika da Miyagu Zuwa Barzahu

Jami'an Tsaro Sun Dakile Harin 'Yan Bindiga, Sun Aika da Miyagu Zuwa Barzahu

  • Ƴan bindiga sun ji a jikinsu bayan sun yi yunƙurin kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma
  • Jami'an tsaro sun yi nasarar daƙile na ƴan bindigan, inda suka hallaka mutum bakwai daga cikinsu tare da raunata wasu da dama
  • Bayan samun nasarr daƙile harin, jami'an tsaron sun kuma ƙwato dabbobi masu yawa da ƴan bindigan suka sace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun hallaka aƙalla ƴan bindiga bakwai bayan sun kai hari a ƙauyen Ruwan Doruwa da ke ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga a Katsina
Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jami'an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

'Yan sa kai sun yi ta'asa a Neja, 'yan sanda sun yi caraf da su

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da makamai sun yi yunƙurin kai hari ne a ƙauyen Ruwan Doruwa, da safiyar ranar Asabar.

Kakakin ƴan sanda ya ce bayan fatattakar ƴan bindigan, an kuma ƙwato shanu 61, tumaki 44, jakuna biyu, akuya guda ɗaya da kare guda ɗaya a yayin artabun.

"A ranar 18 ga Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 9:00 na safe, an samu kiran gaggawa a ofishin ƴan sanda na Dutsinma kan wani hari da wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai irinsu AK-47, suka kai wa ƙauyen Ruwan Doruwa."
"Bayan samun wannan rahoto, DPO tare da sojoji, jami’an DSS, jami'an rundunar KTSCWC da ƴan sa-kai sun gaggauta zuwa wurin da aka kai harin."
"Bayan isarsu wurin, tawagar ta yi ɗauki ba daɗi da ƴan bindigan, wanda ya yi sanadiyyar kashe bakwai daga cikinsu. Ragowar sun tsere ɗauke da raunuka daban-daban, inda suka bar dabbobin da suka sace."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kawo cikas ga ayyukan 'yan Boko Haram da 'yan bindiga

- DSP Abubakar Sadiq Aliyu

Kwamishinan ƴan sanda ya yabawa jami'an tsaro

DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba da ƙwarewa, jarumta da ƙwazon da jami'an tsaron suka nuna.

Ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

“Kwamishinan ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da goyon baya ga rundunar ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka a yaƙin da ake yi da dukkan nau’in laifuka a jihar."

- DSP Abubakar Sadiq Aliyu

Jami'an tsaro sun yi bajinta

Wani mazaunin jihar Katsina mai suna Sahabi Abdulrahman, ya jinjinawa jami'an tsaron kan nasarar da suka samu kan ƴan bindigan.

Ya bayyana Legit Hausa cewa nasarar da jami'an tsaron suka samu abin a yaba ne sosai.

"Gaskiya wannan abin farin ciki ne kuma abin a yaba ne. Muna fatan su ci gaba da samun nasara kan miyagu."

Kara karanta wannan

Harin ta'addanci: 'Yan sanda sun fadi nasarorin da suka samu a Kano

- Sahabi Abdulrahman

Jami'an tsaro sun samu nasara kan ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile yunƙurin ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa a jihar Kebbi d ake yankin Arewa maso Yamma.

Jami'an tsaron sun samu nasarar daƙile harin ne bayan samum sahihan bayanai kan shirin ƴan ta'addan na satar shanu a ƙauyen Gamuzza na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel