Sabuwar Muguwar Kungiya Ta Bulla a Kaduna, An 'Gano' Addinin da Ta Runguma

Sabuwar Muguwar Kungiya Ta Bulla a Kaduna, An 'Gano' Addinin da Ta Runguma

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an samu bullar wata kungiya a jihar Kaduna da aka alakanta da addinin Kiristanci
  • Sabuwar ƙungiya mai suna “ACHAD Life Mission International” ta fara aiki a Arewa maso Yamma, ana zargin tana da alaƙa da fataucin mutane
  • An tabbatar cewa hedikwatar ƙungiyar na Kaduna, yayin da shugabanta, wanda aka bayyana da suna “'Yokana', ke zaune a Jos ta jihar Filato
  • Hukumar Shige da Fice ta NIS ta tabbatar da rahoton sirri da ke nuna cewa ƙungiyar tana amfani da fataucin mutane da raba yara da gidajensu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - An tabbatar da bullar sabuwar ƙungiya mai suna “ACHAD Life Mission International” a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Rahotanni suka ce ƙungiyar tana da alaƙa da fataucin mutane da kuma raba yara da iyayensu.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Wata sabuwar kungiya ta bulla a Kaduna
Rahotanni sun tabbatar da bullar sabuwar kungiya da ake zarginsu da fataucin mutane. Hoto: Legit.
Source: Original

Hukumar NIS ta gano bullar sabuwar kungiya

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ta ce hedikwatar ƙungiyar tana jihar Kaduna, cewar Daily Trust.

Har ila yau, hukumar ta kuma tabbatar da cewa shugabanta, wanda ake kira 'Yokana' na zaune a birnin Jos da ke jihar Filato.

A cikin wata takarda da aka sanya hannu a ranar 14 ga Janairu, 2025, jami’in hukumar CIS A.A. Aridegbe, ya yi kira ga jami’an shige da fice su lura da ƙungiyar.

Hukumar ta ba jami'anta umarni kan yan kungiyar

“An raba bayanai kan bayyanar wata sabuwar ƙungiya mai suna ACHAD Life Mission International”, ga dukkan reshe da cibiyoyin horaswa na hukumar."
"Ana sanar da ku cewa rahoton sirri da muka tattara ya nuna bayyanar wata sabuwar ƙungiya mai suna ACHAD Life Mission International."
“A bisa wannan dalili, ana buƙatar ku kasance masu lura sosai, sannan ku sanar da gaggawa idan kun ga wani alamu, kuma idan zai yiwu ku kama su ku bayar da rahoto.”

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

- Cewar sanarwar

Wani jami’in shige da fice ya tabbatar da ingancin takardar a yau Asabar, yana cewa:

"Eh, mun samu wannan bayanin sirri.”

Ana zargin ƙungiyar da fataucin mutane

Hukumar NIS ta ce akwai rahotanni masu ƙarfi cewa mambobin ƙungiyar suna da alaƙa da fataucin mutane da kuma raba yara da iyayensu.

An gano cewa hedikwatar ƙungiyar na Kaduna, yayin da shugabanta, wanda aka kira ‘Yokana’, ke zaune a Jos da ke jihar Filato, Punch ta ruwaito.

Haka kuma, ƙungiyar ba ta amince da addinin Musulunci ko Kiristanci ba, amma tana wa’azin dawowa kan al’adun Afirka da tallafawa bil’adama.

Rahoton ya ƙara da cewa ƙungiyar tana nemo mambobi daga cikin Najeriya da ma ƙasashen ƙetare, kuma akwai yiwuwar tana da hannu a fataucin mutane.

Sojoji sun magantu kan bullar Lakurawa

Kun ji cewa Rundunar sojojin kasar nan ta tabbatar da shigowar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda daga kasashen Mali da jamhuriyyar Nijar.

Kara karanta wannan

"Babu mai iya girgizamu," Hukumar yaki da rashawa za ta ci gaba da shari'ar Ganduje

Sanarwar da daraktan yada labaran rundunar, Edward Buba ta fitar ta ce yan ta’addan sun yi sansani a Kebbi da Sakkwato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.