Jami'an DSS Sun Nuna Kwarewa, Sun Samu Nasara kan 'Yan Ta'addan Boko Haram
- Jami'an tsaro na hukumar DSS sun samu nasara kan ƴan ta'addan Boko Haram masu mugun nufi a jihar Osun
- Nasarar da jami'an tsaron na DSS suka samu ta sanya sun cafke mambobin ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram
- Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yabawa jami'an tsaron bisa wannan nasarar da suka samu ta cafke ƴan ta'addan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Jami’an hukumar taro ta DSS sun kama mutanen da ake zargin ƴan ta'addan Boko Haram ne a jihar Osun.
Jami'an na DSS sun cafke mutanen guda 10 ne ake zargin mambobin Boko Haram ne a Ilesa da ke jihar Osun.

Asali: Twitter
Malam Olawale Rasheed, mai magana da yawun gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun gwamnan ya ce mutanen da aka cafke mambobin ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne.
Gwamna Adeleke ya yabawa jami'an DSS
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro tare da ba su goyon baya domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Osun.
Gwamna Adeleke ya kuma yi kira ga mazauna jihar da su kasance masu sanya ido kan abin da ke faruwa a unguwanninsu, tare da sanar da hukumomin tsaro idan suka ga wani abu da ba su gamsu da shi ba.
Adeleke ya yabawa ƙoƙarin jami’an tsaro kan yadda suka hanzarta ɗaukar mataki wajen kawar da barazanar ƴan ta’addan, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da zancen.
A cewarsa hakan ya ƙara tabbatar da cewa jami’an tsaro a Najeriya a shirye suke wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
"Gwamnan ya yi matukar jinjina kan yadda jami’an DSS suka tattara bayanan sirri game da ayyukan waɗanda ake zargin, sannan suka yi gaggawar daƙile mummunan aikinsu."
"Wannan ci gaba ne mai kyau kuma abin jin daɗi ne, ba kawai a gare mu a matsayin gwamnati ba, har ma ga mutanen Osun da Najeriya baki ɗaya."
"Na yabawa jami’an tsaro saboda jajircewarsu da kuma yadda suke aiki da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu. Muna da cikakken tabbaci kan jami’an tsaro cewa za su ci gaba da kare mu."
- Sanata Ademola Adeleke
Gwamnatin Osun za ta goyi bayan jami'an tsaro
Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da goyon bayan hukumomin tsaro domin tabbatar da ganin jihar ta kasance cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Haka kuma, ya yi kira ga al’umma da su kasance masu bayar da goyon baya ga jami’an tsaro, ta hanyar bayar da bayanai masu muhimmanci da za su taimaka wajen gano waɗanda ke da niyyar tayar da hankali.
Shugaba Tinubu ya yi naɗi a hukumar DSS
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi sabon naɗi a hukumar tsaro ta DSS.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa mataimakiyar darakta janar ta DSS a karon farko a tarihin hukumar tsaron.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng