Sanusi II Ya Yi Amai Ya Lashe kan Sukar da Ya Yi Wa Gwamnatin Tinubu

Sanusi II Ya Yi Amai Ya Lashe kan Sukar da Ya Yi Wa Gwamnatin Tinubu

  • Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yi martani bayan an taso shi a gaba kan sukar gwamnatin Bola Tinubu
  • Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ba a fahimci kalaman da ya yi ba kan manufofin tattalin arziƙi na shugaban kasa Tinubu
  • Sarkin ya ce kalamansa suna nuna goyon baya ga sauye-sauyen da gwamnatin take yi amma an fahimce su ne a baibai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, ya yi magana bayan ya sha suka kan kalamansa dangane da gwamnatin Bola Tinubu.

Muhammad Sanusi II ya yi ƙarin haske dangane da ce-ce-ku-ce kan kalaman da ya yi kwanan nan dangane da manufofin tattalin arziƙi na shugaba Bola Tinubu.

Sanusi II ya yi magana kan sukar Tinubu
Sanusi II ya ce ba a fahimcu kalamansa ba kan sukar Bola Tinubu Hoto: @DOlusegun, @KyusufAbba
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa an fahimci kalaman nasa ne a baibai, inda aka maida hankali kan wani ɓangare guda kawai na saƙon nasa duk da faɗin da yake da shi.

Kara karanta wannan

"Ba kamar Tinubu ba": Amaechi ya fadi yadda ya shirya samar da sauki ga talaka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Sarkin dai sun haifar da martani daga sassa daban-daban na ƙasar nan, bayan ya bayyana cewa ya zaɓi ka da ya taimakawa gwamnati wajen bayyana amfanin sauye-sauyen da ake aiwatarwa.

Sanusi II ya yi ƙarin haske kan sukar Tinubu

Ya jaddada cewa kalamansa sun nuna goyon baya ga sauye-sauyen gwamnatin, duk da cewa ya amince da sadaukarwar da ƴan Najeriya ke yi saboda matsalolin da aka jima ana fama da su kan tattalin arziƙin ƙasar nan.

"An ɗauki wani ɓangare na magana ta aka cire shi daga muhallinsa, aka mayar da batun abin da zai tada hankula. Ba a duba irin goyon bayan da muka bayar ga gwamnati ba."
"Mun bayyana cewa akwai dalilai masu ƙarfi na goyon bayan waɗannan sauye-sauyen. Mun kuma bayyana cewa muna ji a jiki ne saboda shekaru da dama na rashin kyakkyawan shugabanci kafin mulkin Tinubu."
"Mun kuma ce akwai alamun nasara a nan gaba. Ya kamata mu yi addu’a, mu goyi bayan tsarin, mu kuma tattauna abubuwa masu kyau da ke faruwa.

Kara karanta wannan

'Haba Malam': Hadimin Tinubu ya zargi El Rufa'i da neman rusa gwamnati kan sukar APC

- Muhammadu Sanusi II

Ba a fahimci saƙon Sarki Sanusi II ba

Ya ƙara jaddada cewa jawabinsa ya yi sa ne domin yaƙar sukar da ake yi wa gwamnati a lokacin taron, rahoton Businessday ya tabbatar.

Ya ce kalamansa suna dauke da wani saƙo, amma ba a fahimce su ba, inda ya bayyana cewa ambaton "abokai" da ya yi a gwamnati wani saƙo ne ya tura ga wasu mutane.

"Babu amfani a ci gaba da jan maganar. Ina fatan a nan gaba waɗanda ke cikin gwamnati za su gane cewa na yi magana ne domin su a wurin da ake muhawara ta ilmi."

- Muhammadu Sanusi II

Duk da sukar da kalamansa suka jawo, Sanusi II ya shawarci ƴan Najeriya da su manta da komai, inda ya ce wannan abin mai wucewa ne.

Primate Ayodele ya caccaki shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah ya caccaki shirin rabon tallafin shinkafa na shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Malamin addinin ya bayyana cewa shirin rabon shinkafar babu abin da yake haifarwa sai ƙara yawaitar cin hanci a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel