Sojoji Sun Sake Gurgunta Tasirin Bello Turji a Zamfara, An Yi Masa Mummunan Illa
- Rahotanni sun tabbatar da rundunar sojoji ta ruguza wani ginin makaranta a kauyen Fakai a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya
- An tabbatar cewa an lalata ginin ne da ake amfani da shi wajen adana kayan abinci na shugaban ‘yan bindiga Bello Turji
- Ganin ya kasance ginshikin adana kayan abinci na 'yan bindiga, wanda ke da muhimmanci ga ayyukansu lamarin da ake ganin zai rage musu ƙarfi
- Wannan na zuwa ne yayin da rundunar sojoji ta kara himma domin tabbatar da kakkabe yan ta'adda da suka addabi al'umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Gusau, Zamfara - Rikakken dan ta'adda, Bello Turji ya gamu da matsala bayan lalata wurin adana kayan abincinsa a jihar Zamfara.
An lalata wani ginin makaranta a kauyen Fakai da ake amfani da shi wajen adana kayan abinci na shugaban 'yan bindiga Bello Turji.

Source: Original
Hafsan tsaro ya fadi matsalar ta'addanci a Arewa
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da labarin inda ya ce hakan na daga kokarin hukumomi na kawo karshen ta'addanci a yankin Arewacin Najeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da babban hafsan tsaro kasar nan, Janar Christopher Musa, ya fadi abubuwan da ke kara ta'azzara yaki da ta’addanci a Najeriya.
Janar Musa ya ce talauci, yunwa, da rashin ingantattun ababen more rayuwa suna taimakawa wajen shigar da matasa a cikin kungiyoyin ta’addanci.
Hafsan tsaron ya shawarci gwamnatin Najeriya da sauran makwabtan kasashe a kan yadda za a yi wa matsalar rubdugu domin kawo karshenta.
Yadda aka lalata ma'ajiyar abincin Bello Turji
An lalata kayan abincin da aka tara a wurin gaba ɗaya, lamarin da mayar da ginin ya dawo kango da ake ganin hakan zai jawo wa dan ta'addan matsala.
Daily Post ta bayyana cewa 'yan bindiga sun maida makarantar wajen tallafa wa ayyukansu a wannan yanki.
Ginin ya zama wurin adana kayan masarufi, wanda ke taimaka musu wajen ci gaba da gudanar da ayyukan ta’addanci tsawon lokaci.
Ana hatsashe an kafa rage wa Turji karfi
Rashin wannan wuri yana zama babban koma baya ga rundunar Bello Turji, don kuwa zai dagula tsarin samun kayan aiki da dabarunsu.
Majiyoyi suka ce wannan lamarin ya kara bayyana yunkurin hana tasirin ‘yan bindiga a wannan yanki da mutane da dama suka rasa rayukansu.
Mazauna kauyen Fakai da kewaye na fatan wannan lamari zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tsaron rayuka a yankin.
Bello Turji ya farmaki masallaci a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa hatsabibin ‘yan ta’adda Bello Turji da mabiyansa sun farmaki masallacin Birnin Yaro, Jihar Zamfara yayin da ake tsaka da sallah.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Turji ya sace adadi mai yawa na masu ibada, inda ya mika su cikin daji domin garkuwa da su.
Ana zaton Turji ya kai harin ne saboda rugugin wuta da ya ke sha daga Sojojin Operation fansan yamma a kokarin kawo karshensa yayin da yake addabar mutanen yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

