Mutane Sun Jefa Kansu a Halaka Saboda Abin Duniya, An Rasa Rayuka Sama da 30
- Aƙalla mutane 30 ake fargabar sun mutu, ciki har da wata mata mai juna biyu sakamakon fashewar tankar mai a Dikko Junction a jihar Neja
- A farko tankar ta zubar da mai, lamarin da ya ja mutane suka taru don diban man fetur, wanda daga bisani mummunan gobara ta tashi a wurin
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance amma rahotanni sun nuna cewa jami'an hukumar kwana-kwana sun duƙufa aikin kashe gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Wata babbar tanka maƙare da man fetur ta fashe kuma ta kama da wuta a mahaɗar titin Dikko da ke ƙaramar hukumar Gurara a jihar Neja.
Lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ta zubar da man feturin da ta ɗauko, wanda ya ja hankalin mutane suka yi tururuwa a wurin suna kwasar ganima.

Asali: Original
Jaridar The Nation ta tattaro cewa ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu, wasu kuma sun jikkata ana masu magani a asibitoci daban-daban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana fargabar asarar rayuka 30
Ganau sun bayyana cewa fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane, ciki har da wata mata mai juna biyu da wata matar da ke tare da jaririnta ɗan mako daya.
Rahotanni sun nuna cewa wadanda suka mutu sun fi mutum 30, ko da yake jaridar ba ta tabbatar da wannan adadi kai tsaye ba.
Mutane sun jefa kansu a halaka
An tattaro cewa mummunar gonara ta kama ne a daidai lokacin dautane suka baibaye tankar suna kwasar man feturin da ta zubar, haka. ya sa wutar da rutsa da su.
Gobarar ta bazu cikin kankanin lokaci, inda ta kama wadanda suka taru a wurin da tankar man ta fadi.
Jami'in kwana-kwana sun kai ɗauki
A halin yanzu jami'an hukumar kashe gobara ta jihar Neja na ci gaba da kokarin kashe gobarar, wacce ta yi sanadiyyar konewar wasu motoci da kayayyaki a kusa da wurin.
Duk da haka, har yanzu ana ci gaba da neman karin bayani kan yawan mutanen da suka mutu ko suka jikkata a wannan ibtila'i.
Shaidu a wurin sun ce lamarin ya faru kwatsam, inda tankar man ta fara zubar da mai, sannan mutane suka yi tururuwa don diba ba tare da lura da hatsarin da ke tattare da hakan ba.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga hukumomin gwamnati ko jami’an tsaro dangane da lamarin.
Mutane na ci gaba da jefa ayar tambaya kan yadda ake kula da tankokin mai da kuma irin matakan da za a dauka don hana irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
Gobara ta ƙone kayan kudi a Anambra
A wani rahoton, kun ji cewa ƴan kasuwa sun yi asara mai ɗumbin yawa da gobara ta tashi a wuraren sana'arsu a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabas.
Rahoto ya nuna cewa gobarar ta auku a kasuwar Ahịa Mgbede kuma ta lalata dukiyoyin ƴan kasuwa na miliyoyin Naira.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng