Tsohon Sanata Ya Yi Martani bayan Matatar Dangote Ta Kara Kudin Fetur

Tsohon Sanata Ya Yi Martani bayan Matatar Dangote Ta Kara Kudin Fetur

  • Sanata Shehu Sani bai ji daɗin ƙarin kuɗin man fetur da matatar Dangote ta yi ba a cikin ƴan kwanakin nan
  • Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya nuna takaicinsa kan ƙarin kuɗin da matatar ta yi, inda ya ce ba a yi tsammanin hakan ba
  • Shehu Sani ya nuna cewa tsammanin da aka yi shi ne cewa matatar Dangote za ta sanya farashin man fetur a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan ƙarin farashin man fetur da matatar Dangote ta yi.

Shehu Sani ya nuna takaicinsa kan ƙarin kuɗin da matatar ta yi kan farashin man fetur ɗin da take siyarwa ƴan kasuwa.

Shehu Sani ya koka kan karin farashin fetur
Shehu Sani ya nuna takaici kan karin kudin fetur na matatar Dangote Hoto: @ShehuSani
Source: Twitter

Tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, ya yi martani kan ƙarin kuɗin ne a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano, sun sace diyar babban attajirin dan kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matatar Dangote ta yi ƙarin kuɗin fetur

Matatar Dangote dai ta tabbatar da ƙarin farashin man fetur ga abokan kasuwancinta a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a.

Matatar ta ce masu sayen man fetur tsakanin lita miliyan biyu zuwa miliyan 4.99 za su riƙa siya a kan N955 kan kowacce lita, yayin da masu sayen lita miliyan biyar zuwa sama za su siya a kan N950 kan kowacce lita.

Wannan ƙarin farashin ya nuna an samu ƙarin N55.5, ko kuma kaso 6.17% cikin 100%, idan aka kwatanta da farashin N899.50 kan kowace lita da aka sanar a matsayin rangwame lokacin bikin Kirsimeti a watan Disamba.

Wannan ƙarin farashin zai shafi dukkan ragowar man da ba a ɗauka ba kafin lokacin da aka fara aiwatar da sabon tsarin farashin.

Sanarwar ta ƙara da cewa sabon tsarin farashin zai fara aiki daga ƙarfe 5:30 na yamma a ranar Juma’a, 17 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya fadi wadanda za su iya hana karin kudin kira da data a Najeriya

Dillalan mai sun tabbatar da cewa farashin man fetur zai ci gaba da ƙaruwa, saboda tsadar da ɗanyen mai yake ci gaba da yi a kasuwannin duniya.

Ƙarin farashin ya sanya jama'a na siyan fetur da tsada a yanzu, inda ake sayar da lita ɗaya a tsakanin N1,050 zuwa N1,150.

Me Shehu Sani ya ce kan ƙarin ƙudin fetur?

A martanin da ya yi kan ƙarin farashin, Shehu Sani ya ce ƴan Najeriya sun yi tsammanin cewa matatar Dangote za ta rage farashin mai.

Tsohon sanatan ya bayyana takaicinsa kan ƙarin farashin da matatar ta yi, yana mai cewa wannan ƙarin abin damuwa ne.

"Abin da aka yi tsammani shi ne cewa matatar Dangote za ta rage farashin man fetur, labarin cewa tana ƙara farashin abin takaici ne."

- Shehu Sani

Ba a yi zato ba

Muhammad Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa ƴan Najeriya sun yi fatan samun sauƙi daga wajen matatar Dangote.

Ya bayyana cewa ba a yi zaton sauƙi ba zai samu ba bayan matatar Dangote ta fara aiki.

"Mun yi zaton cewa za a samu sauƙi, amma abubuwan kullum ci gaba kawai suke yi. Allah dai ya kawo mana mafita kawai."

Kara karanta wannan

Maganar N Power ta dawo, Tinubu ya umarci sake fasalinta, matasa za su caɓa

- Muhammad Kabir

Shehu Sani ya magantu kan cushe a kasafin kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya gano hanyar magance yin cushe a kasafin kuɗi.

Shehu Sani ya bayyana cewa hanyar daina yin cushen ita ce a hana ƴan majalisar tarayya a kasafin kuɗin hukumomin gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng