Wasu Matasa Sun Yi Aika Aika a Wurin Bikin Aure, Sun Zama Ajalin Wani Bawan Allah

Wasu Matasa Sun Yi Aika Aika a Wurin Bikin Aure, Sun Zama Ajalin Wani Bawan Allah

  • Dakarun ‘yan sanda sun kama matasa biyar da ake zargin suna da hannu a kisan wani a wurin bikin aure a kauyen Jauro Ali da ke Gombe
  • Mamacin, wanda ya ji raunuka daga dukan da waɗanda ake zargin suka yi masa da sanduna, ya rasu a asibitin Kowa Clinic da ke Tongo
  • Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce bincike ya yi nisa kan lamarin kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi da zarar an kammala bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe - Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama matasa biyar da ake zargin suna da hannu a mutuwar wani bawan Allah a kauyen Jauro Ali.

An ruwaito cewa waɗanda ake zargin sun lakaɗawa matashin dukan kawo wuƙa bayan wata gardama ta haɗa su a wurin bikin aure.

Kara karanta wannan

IPOB ta sako Sheikh Gumi a gaba bayan shawarsa a kan ta'addanci

Yan sandan Najeriya.
Yan sanda sun kama matasa 5 bisa zargin kisan wani bawan Allah a taron bikin aure Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Matasa 5 da ƴan sanda suka damƙe

Jaridar Punch ta tattaro cewa an bayyana sunayen waɗanda ake zargin da suka haɗa da Jauro Babawuro (17), Yayaji Bello (16) da Baffaji Adamu (16),

Sauran su ne Babangida Dotti (18), da Yaya Bapati (17), kuma an kama su bayan mahaifin mamacin, Dotti Manu daga kauyen Wuro Wandara, ya kai rahoto ga ‘yan sanda.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Gombe, Buhari Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne ranar 21 ga watan Disamba, 2024 da misalin ƙarfe 10:00 na dare.

Rahotanni sun bayyana cewa a wurin shagalin bikin auren, rigima ta shiga tsakanin waɗanda ake zargi da mamacin, wanda ya kai ga suka masa rubdugu da sanduna.

Mutum 5 sun lakaɗawa wani duka har lahira

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce:

“Mahaifin mamacin ya kawo mana rahoton cewa a ranar 21 ga Disamba, 2024, da misalin karfe 10:00 na dare a wurin taron murnar aure, gardama ta barke tsakanin dansa da waɗanda ake zargi.

Kara karanta wannan

"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

"Wanda hakan ya sa suka tarar wa dansa, suka doke shi da sanduna, ya samu munanan raunuka a ciki."

Buhari Abdullahi ya ce bayan haka aka kwantar da mutumin a asibitin Kowa Clinic aka fara ƙoƙarin yi masa magani amma daga bisani Allah ya masa rasuwa.

Yan sanda sun fara gudanar da bincike

Bayan ya rasu, an kai gawarsa babban asibitin Bajoga domin gudanar da binciken gawa wanda zai taimakawa ƴan sanda..

“Muna kan Bincike game da lamarin kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike,” in ji Abdullahi.

Rundunar ‘yan sanda ta kuma bukaci duk wanda ke da wata masaniya kan lamarin da ya zo ya gaya mata abin da ya sani.

“Muna da yakinin ganin cewa an yi adalci a wannan lamari, kuma za mu tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata laifin,” in ji shi.

Mutum 1 ya mutu a faɗan matasa da makiyaya

A wani labarin, kun ji cewa faɗa ya kaure tsakanin matasa da makiyaya a yankin ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan ta'adda ya kai ziyarar jaje gidan mutanen da ya yi garkuwa da su

Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutum ɗaya a rikicin wanda ya samo asali daga tare hanyar da matasa suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262