Abuja: Fadar Shugaban Kasa za Ta Shiga Duhu, An Sace Manyan Kayan Wutar Lantarki

Abuja: Fadar Shugaban Kasa za Ta Shiga Duhu, An Sace Manyan Kayan Wutar Lantarki

  • TCN ta tabbatar da cewa wasu bata-gari sun lalata layukan wutar 132kv na karkashin kasa da ya jawo katsewar wuta
  • Lamarin ya shafi yankunan Maitama, Wuse, Jabi, Lifecamp, Asokoro, Utako, Mabushi, da wani bangare na Fadar Shugaban Kasa
  • TCN ta aika tawagar injiniyoyi domin gyara lalacewar cikin kankanin lokaci, tare da yin kira ga al’umma su sanya ido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa wasu bata-gari sun sake kai hari kan layukan wutar lantarki a Abuja. A wata sanarwa da Ndidi Mbah, mai magana da yawun kamfanin, ta fitar, ta ce lamarin ya faru a farkon safiyar Juma’a, kuma ya shafi sassa daban-daban na Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Kamfani
An sace kayan wuta a Abuja Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa harin ya shafi layin wuta na 132kv da kebul na karkashin kasa da ke rarraba wuta zuwa tashar rarraba wuta ta 132kv Central Area substation da ke Katampe, Abuja.

TCN: Za a fuskanci rashin wutar lantarki

Sanarwar TCN ta kara da cewa harin ya shafi tashoshin rarraba wutar lantarki guda takwas da ke bai wa yankin Central Area wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce hakan ya janyo katsewar fiye da kashi 60% na wutar lantarki a yankunan Maitama, Wuse, Jabi, Lifecamp, Asokoro, Utako, Mabushi da wani bangare na Fadar Shugaban Kasa.

Sanarwar ta ce:

“Hakan ya shafi yankuna kamar Maitama, Wuse, da Garki,”

TCN ta koka da lalata kayan wuta

TCN ya koka kan yawaitar lalata kayayyakin wutar lantarki a fadin kasa, inda ta ce ta aika tawagar injiniyoyi zuwa wurin da abin ya faru domin ganin an gyara lalacewar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi yadda aka zuba jarin $6.7bn a bangaren makamashi

Mai magana da yawun TCN ta bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa su yi hakuri, tana mai cewa ana ci gaba da kokarin dawo da wutar cikin kankanin lokaci.

Ta ce:

“Masu lalata kayan wutar sun kai harin ne a kusa da yankin Menillum Park a Abuja.”

TCN: An sace kayan wutar lantarki

Kamfanin ya bayyana cewa masu lalatar sun sace layin wuta mai tsawon 40 meters na 1x500mm conductor daga layukan wutar 132kv guda biyu. Kamfanin ya ce injiniyoyinsa sun fara aiki a wurin domin dawo da layukan wutar da aka lalata, sannan ya yi kira ga 'yan Najeriya su rika sanya ido don kare kayan aikin wutar lantarki. A bara, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta kashe Naira biliyan 8.8 wajen gyara turakun wutar lantarki guda 128 da aka lalata a fadin kasar nan daga ranar 20 Janairu zuwa 28 Nuwamba.

"An lalata babban layin wuta," TCN

Kara karanta wannan

2027: Tsofaffin gwamnnonin PDP 5 da za su iya goyon bayan Tinubu idan ya nemi tazarce

A wani labarin, mun wallafa cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da lalacewar layin wutar lantarki na 330kV daga Shiroro zuwa Katampe.

A wata sanarwa da Ndidi Mbah, jami'in hulda da jama'a na TCN, ya fitar, an bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Laraba da misalin karfe 11:43 na daren Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.