'Mun Amince, amma da Sharadi': Gwamnoni 36 Sun Dauki Matsaya kan Gyaran Haraji
- Gwamnonin Najeriya sun yi watsi da ƙarin harajin VAT don tabbatar da daidaiton tattalin arziki da jin daɗin jama'a a kowace jiha
- Gwamnonin sun gabatar da sabuwar hanyar rabon VAT yayin da suka amince da kudurin Shugaba Bola Tinubu na gyaran haraji
- A wani zama da suka yi, gwamnonin sun goyi bayan ci gaba da samar da haraji ga hukumomin ƙasa kamar NITDA, TETFund
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnonin Najeriya 36, karkashin kungiyar NGF, sun gabatar da sabuwar hanyar rabon harajin VAT.
NGF ta bayyana cewa ta gabatar da hanyar ne domin magance damuwar gwamnoni game da tsarin gyaran harajin Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Gwamnoni sun yi watsi da harajin VAT
A wata sanarwa da hadimin Bola Tinubu, Olusegun Dada ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, gwamnonin sun yi watsi da karin VAT.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin ganawarsu da kwamitin gyaran haraji a Abuja, gwamnonin sun ce ba za su iya amincewa da karin hajin VAT a halin yanzu ba.
Gwamnonin sun jaddada bukatar kiyaye daidaiton tattalin arziki da tabbatar da jin daɗin jama'a yayin gyare-gyaren tattalin arzikin Shugaba Tinubu.
Kungiyar NGF ta ba da shawarar ci gaba da keɓance kayan masarufi da amfanin gona daga harajin VAT don kiyaye walwalar 'yan ƙasa da haɓaka yawan amfanin gona.
Gwamnoni sun kawo sabon tsarin rabon haraji
A wajen taron, gwamnonin sun amince da tsarin raba harajin VAT don tabbatar da rarraba albarkatu cikin adalci kamar haka:
- Raba kaso 50 daidai wadaita tsakanin jihohi.
- Raba kaso 30 gwargwadon harajin da kowacce jiha ta tara.
- Raba kaso 20 gwargwadon yawan al'ummar kowacce jiha.
A cewar Abdulrahman Abdulrasaq, shugaban kungiyar NGF kuma gwamnan jihar Kwara, sabuwar hanyar rabon VAT za ta taimaka wajen tabbatar da daidaito a raba albarkatu.

Kara karanta wannan
Kungiya ta gano sabuwar matsala a rabon harajin VAT, an gargadi gwamnonin Najeriya
An fitar da matsayar gwamnonin da sa hannun Mai girma Abdulrahman Abdulrasaq a shafin X.
Majalisa za ta ci gaba tsara kudurorin haraji
Gwamnonin sun kuma nuna goyon bayansu ga ci gaba da tsarin dokokin haraji a majalisar tarayya har zuwa lokacin zartar da kudurorin.
Sun kuma goyi bayan cewa a bar haraji da aka ware wa wasu hukumomin ƙasa.
Hukumomin da aka goyi bayan a ci gaba da samarwa kudi sun hada da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), TETFund da NASENI.
Taro kan batun kudirin haraji a Abuja
A ranar Alhamis aka samu labari cewa da alama zZa a shafe kwanaki ana tattaunawa game da kudirin gyaran haraji da gwamnati ta bijiro da shi.
Kwamitin kudirin haraji ya gana da manyan jami'an gwamnati a Abuja. Shugabanni a matakin kasa da jihohi ne suka hadu domin fahimtar juna.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
