Gwamna Radda Ya Sha Alwashi bayan 'Yan Bindiga Sun Farmaki Ma'aikatan Lafiya
- Gwamnan jihar Katsina ya nuna takaicinsa kan harin ta'addanci da ƴan bindiga suka kai a babban asibiti da ke ƙaramar hukumar Kankara
- Dikko Umaru Radda ya bayyana harin a matsayin mugun nufi mai cike da zalunci kan marasa lafiya da ma'aikatan lafiya
- Gwamna Radda ya sha alwashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan ƴan bindigan da suka kai harin, inda ya ce ko kaɗan ba za a ɗaga musu ƙafa ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya yi magana da kakkausar murya kan harin da ƴan bindiga suka kai a Kankara.
Gwamna Dikko Radda ya sha alwashin ɗaukar mataki mai tsauri kan ƴan bindigan da suka kai harin, kan marasa lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya a babban asibitin Kankara.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammad ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya yi tir da harin ƴan bindiga
Gwamna Radda ya yi tir da harin ƴan bindigan, inda ya bayyana shi a matsayin mummunan nufi kan marasa lafiya da cibiyoyin kiwon lafiya.
Gwamnan ya bayyana shirinsa na ɗaukar ƙarin matakan tsaro, wanda ya haɗa da tura ƙarin jami’an tsaro zuwa cibiyoyin kiwon lafiya a faɗin jihar.
“Wannan hari kan ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya ya nuna yadda waɗannan ƴan ta’adda suka zama marasa tausayi masu zalunci."
“Duk da cewa mun samu ci gaba wajen rage irin waɗannan hare-hare, wannan lamari ya tunatar da mu cewa har yanzu muna da sauran aiki a gabanmu."
“Gwamnatin Katsina ba za ta bari miyagu su hana damar samun kiwon lafiya ko su jefa rayukan ma’aikatan lafiya cikin hatsari ba."
"Duk wanda aka samu yana taimakawa waɗannan miyagun ko kuma yana da hannu a irin waɗannan hare-hare zai fuskanci hukunci mai tsanani."
"Ba za mu ɗaga ƙafa ga waɗanda ke barazana ga ɓangaren kiwon lafiyarmu ba."
- Dikko Umaru Radda
Radda zai kare ma'aikatan lafiya
Gwamnan ya kuma tabbatarwa da ƙungiyar likitoci ta Najeriya (NMA) reshen jihar Katsina da kuma ma’aikatan asibitin da abin ya shafa cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare lafiyar su.
Ya jaddada cewa kare ma’aikatan kiwon lafiya da mazauna jihar na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali a kai.
Jami'an tsaro sun kashe shugaban ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro da suka haɗa da sojoji, ƴan sa-kai da na rundunar KSWC sun samu gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ƴan bindiga a jihar Katsina.
Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban ƴan bindiga bayan sun gwabza faɗa da mayaƙansa a ƙaramar hukumar Batsari.
An samu wannan gagarumar nasarar ne bayan farmakin haɗin gwiwa da jami'an tsaron suka kai kan maɓoyar shugaban ƴan bindigan, mai suna Bako Bako.
Asali: Legit.ng