Yadda Dakarun Sojoji Suka Hallaka 'Yan Ta'adda Kusan 200 yayin Artabu
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu nasarori masu yawa a sassaɓ daban-daban na ƙasar nan
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 156 da cafke wasu 464 a cikin mako guda
- DHQ ta bayyana cewa dakarun sojojin sun kuma ƙwato tarin makamai da suka haɗa da bindigu da alburusai daga hannun ƴan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojoji suka samu a kan ƴan ta'adda a cikin mako guda.
DHQ ta bayyana cewa dakarun sojoji sun kashe ƴan ta'adda 156, sun kama wasu 464, sannan sun ceto mutane 181 da aka yi garkuwa da su cikin mako guda.
Babban daraktan watsa labarai na DHQ mai barin gado, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin jawabin bankwana a Abuja, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a cikin wannan lokacin, dakarun sun kama mutane 29 da ake zargi da satar man fetur, tare da ƙwato kayayyakin da darajarsu ta kai Naira miliyan 623,447,390.00 kacal.
Sojoji sun ƙwato makamai a hannun ƴan ta'adda
Manjo Janar Edward Buba ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun ƙwato makamai guda 219 da harsasai guda 2,871 a cikin mako guda.
Ya ce makaman da aka ƙwato sun haɗa da, GPMG guda daya, bindigogin AK47 guda 68, bindiga ƙirar AK56 guda daya, bindigogi 12, bindigogin FN guda huɗu, manyan bindigu bakwai, RPG guda shida, jigida 27, da sauransu.
Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da harsasai 1,618 masu kaurin 7.62mm, harsasai 676 na NATO masu kaurin 7.62mm, harsasai 16 masu kaurin 7.62 x 51mm, harsasai 68 masu kaurin 7.62 x 39mm, da sauransu.
Ya ce dakarun sojojin sun kuma ƙwato rediyon baofeng guda ɗaya, motocin guda 10, babura 42, wayoyi 29, da sauran abubuwa.
Sojoji sun ragargaji ɓarayin mai
A yankin Neja Delta, dakarun sun gano tare da lalata haramtattun wuraren tace mai guda 46, murhunan girka ɗanyen mai guda 48, ramuka guda 10, da wuraren ajiyar mai guda 56.
Bugu da ƙari, dakarun sun kwato lita 705,294 na ɗanyen mai, lita 6,865 na AGO, lita 1,500 na DPK da lita 800 na man fetur.
Sauran kayayyakin da aka ƙwato a wannan yanki sun haɗa da kwale-kwale guda 28, injina guda takwas, babura guda takwas, waya guda ɗaya da motoci guda takwas da sauransu.
"Duk da cewa dakarun na iya fuskantar wasu koma baya a lokaci bayan lokaci, wanda hakan abu ne da zai iya faruwa a duk wani fagen yaƙi, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba kan burin mu na karya ƙarfin gwiwar ƴan ta'adda."
- Manjo Janar Edward Buba
Ƴan ta'adda sun farmaki sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun fuskanci harin kwanton ɓauna daga wajen tsagerun ƴan ta'adda a jihar Borno.
Sojojin dai sun je ɗauko gawarwakin manoman da ƴan ta'addan suka kashe ne, sai kawai suka faɗa tarkon da miyagun suka ɗana musu.
Asali: Legit.ng