'Ana Fargabar Jami'ai 53 Sun Bace': Yadda 'Yan Ta'adda Suka Farmaki Sojoji a Borno
- 'Yan ta'adda sun kai wa sojoji da 'yan sa-kai hari yayin da suke kwaso gawarwakin manoma 40 da aka kashe a jihar Borno
- Ana fargabar sojoji da 'yan CJTF sun rasa jami'ai da dama yayin harin ISWAP, wasu kuma sun bata ko sun fada hannun 'yan ta'addan
- Wasu majiyoyin tsaro sun yi bayanin yadda 'yan ta'adda suka yiwa sojoji da jami'an hadin guiwar kwanton bauna a yankin Dumba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'adda sun kai wa sojoji da fararen hula hari yayin da suke kan aikin kwaso gawarwakin manoma 40 da aka kashe a Dumba.
Wannan al'amari ya faru a yankin Baga, karamar hukumar Kukawa, jihar Borno, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana jiya Laraba.
'Yan ta'adda sun farmaki sojoji a jihar Borno
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa mayakan ISWAP ne suka kai harin, suka jefa sojoji da 'yan sa-kai cikin halin 'tsaka mai wuya.'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa wasu daga cikin sojoji da mutum 54 na kungiyar CJTF ba su dawo ba har yanzu.
Wani mamba na CJTF ya ce daga cikin jami'an tsaro 54 da aka tura aikin, mutum daya ne kawai ya dawo cikin garin Baga.
Ya bayyana cewa sojojin sun yi kokarin fatattakar 'yan ta'addan, amma sun fi karfinsu saboda yawan makamai da 'yan ta'addan ke da shi.
Ana fargabar jami'an tsaro sun bata a Borno
Dangane da adadin wadanda ake fargabar an rasa, ya ce:
"Har yanzu ba a tabbatar ba saboda wanda ya dawo ba ya cikin yanayi hayyacinsa balle ya yi bayani."
A hannu daya kuma, wata majiyar tsaro ta ce wasu daga cikin sojojin da aka tura sun tsira kuma sun koma sansaninsu.
Majiyar ta kara da cewa sojojin sun gamu da harin ne sun tsaka da tafiya bayan sun kwaso gawarwakin wasu manoma tare da birne 15.
“Sun ga wasu gawarwaki a kan hanya, amma suka yi kokarin ci gaba da tafiya zuwa garin Dumba, inda a hanyar ne 'yan ta'addan suka farmake su.
“Da yawa daga cikin sojoji da 'yan sa-kai sun bata tun ranar Talata. Ba mu san ko sun bata a daji ko kuma sun shiga hannun 'yan ta'adda ba."
- A cewar majiyar.
Sojoji da 'yan ta'adda sun yi musayar wuta
Wani jami'in CJTF ya ce:
“Lamarin na cike da tashin hankali. Ba zan iya fadi adadin wadanda suka bata ba, amma muna fatan za su dawo lafiya.”
“Akalla mutane 70 na cikin tawagar ceton, amma 'yan kadan ne suka dawo. Sun gano gawarwaki fiye da 60, amma sun birne 15 kacal."
Wani mai kamun kifi ya ce sojoji da 'yan ta'addan sun yi musayar wuta jiya da yamma.
“Na ga jiragen yaki suna shawagi suna goyon taimakawa sojojin da ke kasa suna musayar wuta da 'yan ta'adda. Sai muka tsere don tsira da rayukanmu,” inji masuncin.
Manoman Baga sun roki gwamnatin Borno da ta mayar da su wurare masu aminci har sai an tabbatar da tsaro a yankunansu.
Zulum ya roki sojoji su murkushe 'yan ta'adda
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan ta'adda sun hallaka manoma 40 a Dumba, yayin da wasu suka tsere, har yanzu ana ci gaba da neman wasu da suka bata.
Gwamna Babagana Zulum ya jajanta wa iyalan mamatan, yana rokon sojoji su murkushe 'yan ta'adda, ya gargadi jama'a su guji fita daga yankunan da aka killace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng