Kaya Sun Kara Tsada a Kasuwa, Tinubu Ya Ce Manufofinsa Sun Fara Haifar da Mai Ido
- Mai girma Bola Tinubu ya jaddada cewa canje-canjen tattalin arzikin da Najeriya ta aiwatar suna samar da sakamako mai kyau
- Ya ce wannan ne ya ja hankalin masu zuba jari daga kasashen waje, ciki har da kamfanonin mai na duniya zuwa kasar
- Shugaba Tinubu ya gayyaci takwaransa na UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan don ganin yadda Najeriya ta ke
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana ce tattalin arzikin Najeriya ya na habaka, domin canje-canjen tattalin arzikin a kasar sun fara samar da sakamako mai kyau.
Ya kuma yi kira ga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da ta hada kai da Najeriya domin inganta tattalin arzikin kasar da kara kulla alakar kasuwanci.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin X cewa Bola Tinubu ya bayyana cewa an fara ganin sakamakon manufofin da gwamnatinsa ta dauka a fannin tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya bayyana cewa canje-canjen sun tabbatar da dorewar tattalin arzikin yayin da rahoton hukumar kididdiga ta kasa ke nuna an samu hauhawar farashi.
UAE ta amince da tayin Bola Tinubu
Arise News ta ruwaito cewa Shugaban UAE, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya amince da gayyatar shugaba Tinubu na ziyarar Najeriya a wannan shekarar.
Wannan ya biyo bayan gayyatar da Tinubu ya yi masa yayin taron hadin gwiwa na Najeriya da UAE a yayin bikin Abu Dhabi Sustainability Week 2025 da ke gudana a yanzu.
Tinubu ya isa Abu Dhabi a ranar Lahadi a matsayin bakon Shugaban kasar UAE domin halartar taron don musayar ra'ayoyi da zai tallafawa ci gaba mai dorewa a duniya.
Sauyin yanayi: Tinubu ya fadi matsayar Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matsayin Najeriya kan sauyin yanayi da sauran kalubale, inda ya ke fatan a shawo kan matsalolin da su ka addabi duniya.
A yayin tattaunawarsa da Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya gode wa shugaban Najeriya bisa amincewar sa da gayyatar da aka yi masa, tare da nuna nufin karfafa alaka.
Shugaba Tinubu ya gode wa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan bisa girmamawa da kuma tarbar da tawagar sa cikin karamci tun bayan isowar su a karshen mako.
Tawagar Tinubu zuwa kasar UAE
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; Ministan Kudi, Wale Edun; da Babban Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, sun kasance tare da Tinubu a wannan taro.
Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, Mataimakin Firayim Minista da Ministan Harkokin Waje na UAE; Sheikh Hamdan bin Mohamed bin Zayed Al Nahyan sun halarci taron.
Sauran jami'an UAE da su ka halarci taron sun hada da: Reem bint Ebrahim Al Hashimy da Minista mai kula da Hadin Gwiwar Kasa da Kasa; Dr. Sultan bin Ahmed Al Jaber.
Shugaban Najeriya, Tinubu ya kafa tarihi
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa tarihi tare da yin wani muhimmin naɗi mai jan hankali kuma irinsa na farko a hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Folashade Arinola Adekaiyaoja, ƴar asalin jihar Kogi, a matsayin mataimakiyar darakta janar ta DSS, lamarin da ya fara samun karbuwa matuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng