Gwamnoni, Shugaban Majalisa Sun Shiga Jerin Mutane 565 da Wike Ya Kwace Filayensu a Abuja

Gwamnoni, Shugaban Majalisa Sun Shiga Jerin Mutane 565 da Wike Ya Kwace Filayensu a Abuja

  • Wasu daga cikin manyan kasar nan, ciki har da gwamnoni, shugaban majalisar wakilai, Abbas Tujudeen sun rasa filayensu a Abuja
  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kuma ba da umarnin kwace filayen wasu tsofaffi da kuma masu rike da mukamai a majalisar tarayya
  • Ya ce an dauki matakin ne saboda mutanen sun yi kunnen kashi wajen biyan kudin mallakar filayensu a Abuja kafin wa'adi ya cika

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnan Imo, Hope Uzodimma da na Bayelsa, Douye Diri, da Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, sun shiga komar Nyesom Wike.

Sabon umarnin da Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya bayar ya tabbatar da kwace filayen fitattun 'yan siyasan saboda taurin bashi.

Kara karanta wannan

Kaya sun kara tsada a kasuwa, Tinubu ya ce manufofinsa sun fara haifar da mai ido

Nyesom
Wike ya kwace filaye sama da 500 a Abuja Hoto; Abbas Tajudeen/Nyesom Ezenwo Wike/@ShehuSani
Asali: Facebook

Manya sun rasa filayensu a birnin Abuja

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wadanda abin ya shafa sun hada da Mataimakin shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa), Ibrahim Hadejia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele; Shugaban ‘Yan Adawa na Majalisar Dattawa, Abba Moro; da Ministar Kasuwanci da Zuba Jari, John Eno.

Wike ya kwace filayen 'yan majalisa

Solacebase ta ruwaito Ministan ya kuma ba da umarnin kwace filayen wasu tsofaffi da kuma masu rike da mukamai a Majalisar Dokoki ta Kasa.

Wadanda abin ya shafa sun hada da Shehu Sani, Magnus Abe, David Umaru, Lanre Tejuoso, Oluwole Oke, da Lynda Ikpeazu.

Sauran sun hada da Orker Jev, Agom Jarigbe, Nicholas Mutu, Gilbert Nnaji, Francis Onyewuchi, da kuma Hon. Abubakar Fulata.

Haka kuma, wasu 'yan uwan tsohon Alkalin Alkalai na Najeriya guda 2 sun rasa filayensu.

Kara karanta wannan

Ana shirin ƙara farashin fetur a Najeriya, NNPCL ya tara wa gwamnati Naira tiriliyan 10

Kamfanonin da Wike ya kwacewa filaye

Wasu kamfanoni da abin ya shafa sun hada da Abuja Enterprise Agency, Silver Proof Nigeria Limited, Sali-Tech Commercial Limited,.

Sauran sun hada da Gimag Integrated Services Limited da Earth Conscience Limited, duka bisa zargin kin mutunta wa'adin da aka ba su.

Dalilin Wike na kwace kadarorin jama'a

A cewar sanarwar da Hukumar gudnarwar Abuja ta fitar a ranar Laraba, an kwace filayen 568 saboda kin biyan kudin takardar shaidar mallaka har wa'adin 15 Janairu, 2025 ya wuce.

Sanarwar tacce;

“A bisa tanadin dokar amfani da filaye ta 1978, FCTA ta sanar da duk masu filaye a Maitama II, Cadastral Zone A10, Abuja, cewa wadanda suka gaza biyan kudaden takardun shaidarsu bayan karewar wa’adin da Ministan Abuja ya bayar, an kwace musu filayensu.”
“Dukkan wadanda suka kammala biyan kudinsu kafin 15 Janairu, 2025, ba su cikin wadanda wannan hukuncin ya shafa.”

Kara karanta wannan

Tsohon Sanata, Shehu Sani ya fadi silar lalacewar lamura a Najeriya

Nyesom Wike ya kara da tabbatar da cewa sai wadanda ake bi kudin filayen sun sauki nauyin da ke kansu kafin a sake mallaka masu dukiyoyinsu.

Shugaban majalisa ya gargadi Wike

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya karyata rahotanni da ke yawo na cewa filayensa na daga cikin wanda Nyesom Wike ya kwace.

A cikin wata sanarwa daga hadiminsa, Abbas ya gargadi Hukumar FCTA da ta rika taka tsan-tsan wajen gudanar da ayyukanta, ya kuma gargadi kafafen yada labarai a kan yada karya ga jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.