ICPC Ta Sake Cafko Wani Mutumin El Rufa'i, Za a Tafi Kotu da Shi kan Zargin Rashawa
- Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta zargi Jimi Lawal da karbar miliyoyin Naira daga asusun gwamnatin jihar Kaduna
- ICPC ta ce tsohon hadimin gwamna Nasir El Rufa'i ya karbi akalla Naira miliyan 10 daga Asusun Akanta Janar na Kaduna
- Ta yi zargin ya rika tura kudaden zuwa asusun GTB na kamfanin Solar Life Nigeria Limited wanda shi ne ya mallaki akawun din
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta kasa (ICPC) ta sake tuhumar wani tsohon ma’aikacin gwamnatin jihar Kaduna kan zargin rashawa.
ICPC ta gabatar da tuhume-tuhume guda biyar a kan Jimi Lawal, tsohon hadimin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bisa zargin rashawa da kuma halasta kudin haram.
The Cable ta ruwaito cewa Jimi Lawal ya na babban mai ba da shawara ga tsohon gwamna El Rufa'i, kuma ya zama daga cikin 'yan kwamitin bunkasa tattalin arzikin Kaduna daga 2019 zuwa 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC, ta hannun jami’inta mai kula da shari’a, Osuobeni Akponimishingha, ta shigar da karar mai lamba FCH/KD/16c/2025 a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Laraba.
Za a yi shari’a da tsohon hadimin El-Rufa’i
Jaridar Business Day ta ruwaito cewa za a gurfanar da Jimi Lawal a kan tuhume-tuhume guda uku tare da wasu mutane uku: Umar Waziri, Yusuf Inuwa da kamfanin Solar Life Nigeria Limited.
A tuhume-tuhumen da aka gabatar, ICPC ta zargi Jimi Lawal da cewa;
“A wani lokaci a shekarar 2018, ya karbi kudiNaira miliyan 10 daga asusun Akanta Janar na jihar Kaduna mai lamba 0211139802 ta hanyar tsarin Guaranty Trust Bank Automated Payment System (GAPS) sannan ya tura kudaden zuwa asusun bankin Guaranty Trust Bank mai lamba 0130133086, wanda na kamfanin Solar Life Nigeria Limited ne, kuma shi kadai ne ke iya sarrafa asusun.:
An zargi tsohon gwamna El Rufa’i da rashawa
A tuhume-tuhuma ta biyu, an zargi Lawal da cewa ya karbi N47.8m daga ma’aikatar kudin jihar Kaduna ta hanyar asusun bankin GTB mai lamba 0130133086 a watan Yuli 2018.
Haka zalika, hukumar ta zargi cewa a watan Satumba na 2018, Lawal ya karbi N7.3m daga asusun kudaden shiga na cikin gida na jihar Kaduna.
ICPC ta soki tsohon hadimin gwamnan Kaduna
ICPC ta ce ya kamata Jimi Lawal ya san cewa kudaden sun fito ne daga wata haramtacciyar hanya ta cin hanci, wanda ya saba wa sashe na 18(2)(d) na dokar yaki da rashawa na 2022.
A tuhume-tuhuma ta uku, ICPC ta zargi cewa a watan Oktoba 2024, Lawal ya ba da bayanan karya ga masu bincike, Messrs Wellington Nkemadu da Gudi Johnson Daniel.
Hukumar ta ce;
“Lawal ya san cewa wannan ikirari karya ne, wanda ya saba wa sashe na 25(1)(a) kuma abin hukunta ne a karkashin sashe na 25(1)(b) na dokar yaki da cin hanci ta shekarar 2000.
Kotu ta hana belin tsohon hadimin El Rufa'i
A baya, mun ruwaito cewa babbar kotun jihar Kaduna ta ki amincewa da belin Muhammad Bashir Sa'idu, tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tsohon gwamnan Kaduna.
An kama Sa'idu ne a ranar 30 ga Disamba, 2024, a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, sannan aka gurfanar da shi a gaban babbar kotun majistare da ke Rigasa, inda ake tuhumarsa da rashawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng