Dakarun Sojoji Sun Yi Bajinta, Sun Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Masu Yawa
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'adda a jihohin Kebbi da Sokoto na yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun yi nasarar hallaka ƴan ta'addan masu yawa a farmakin da suka kai musu a maɓoyarsu
- Jami'an tsaron sun ƙwato makamai tare da lalata kayayyaki masu yawa na ƴan ta'addan bayan sun samu nasara a kansu a gumurzun da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Dakarun Sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yamma sun farmaki ƴan ta'adda a jihohin Sokoto da Kebbi.
Dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan ta'addan a hare-haren da suka kai musu.
Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kai hare-hare maɓoƴar ƴan ta'adda
Sojojin sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomi Illela, Tangaza, Gudu, Binji, da Silami a jihar Sokoto, da Augie, Arewa, Argungu, da Dandi a jiihar Kebbi.
A yayin farmakin dakarun sojojin sun kashe fiye da ƴan ta’adda 20, sun lalata sansanoninsu, kuma sun tilasta musu tserewa daga maɓoyarsu.
Hare-haren waɗanda aka shirya don dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa, sun sanya dakarun suna kutsawa cikin maɓoyar ƴan ta’adda a ɗazukan Tsauna, Bauni da Sarma.
Dakarun sun shiga cikin maɓoyar miyagun, inda suka riƙa fatattakar ƴan ta’addan, suna lalata sansanoninsu sannan suka ƙwato kayan aiki.
A ƙauyen Sarma Ruga, dakarun sojojin sun kashe ƴan ta’adda 20 a gumurzun da suka yi.
Ƴan ta’addan sun tsere sun bar makamai da kayayyakinsu, waɗanda dakarun sojojin suka lalata daga baya.
Sojoji sun ƙwato ƙauyen da ya daɗe ba mutane
Wani babban ci gaba shi ne tsaftace ƙauyen Manja, wanda aka barshi babu kowa har na tsawon shekaru huɗu saboda ayyukan ƴan bindiga da ƴan ta’adda.
Abin farin ciki, mazauna ƙauyen sun fara dawowa gidajensu, suna nuna farin ciki tare da godiya ga sojojin Najeriya da suka fatattaki ƴan ta'adda a yankin.
Waɗannan nasarori na nuna jajircewa da ƙwarewar sojojin Najeriya wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankunan Arewa maso Yamma na Najeriya.
Sojoji sun hana amfani da jirage marasa matuƙa
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai ta haramta yin amfani da jirage marasa matuƙa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Kwamandan sashen sama na rundunar wanda ya sanar da haramcin yin amfani da jiragen, ya bayyana cewa suna haifar da barazana ga ayyukan taaro a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
Air Commodore U.U. Idris wanda ya koka kan yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke amfani da jiragen ba bisa ƙa'ida ba, ya ce za a ɗauki mataki kan duk wanda ya karya dokar.
Asali: Legit.ng