Jami'an Tsaro Sun Ƙara Kama Mahdi Shehu a Asibiti, Iyalansa Sun Yi Magana

Jami'an Tsaro Sun Ƙara Kama Mahdi Shehu a Asibiti, Iyalansa Sun Yi Magana

  • Jami’an tsaro da ake zargin dakarun hukumar DSS ne sun ƙara kama ɗan gwagwarmaya, Mahdi Shehu a Unguwar Dosa da ke Kaduna
  • Har yanzu hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan kama Mahdi Shehu ba, kuma iyalansa sun ce ba su ji ta bakinsa ba
  • A baya, an kama Mahdi Shehu a watan Disamba 2024 tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya kan wallafa bidiyo da ake zargin yaudara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Jami’an tsaro da ake zargin na hukumar tsaron farin kaya watau DSS ne sun sake kama ɗan gwagwarmayar nan, Mahdi Shehu a Kaduna.

Wannan kame na biyu da aka yi wa Mahdi Shehu cikin ƴan watanni na zuwa ne makonni ƙalilan bayan kotu ta bayar da belinsa.

Mahdi Shehu.
Jami'an tsaro sun sake damƙe Mahdi Shehu a jihar Kaduna bayan kotu ta ba da belinsa Hoto: @Shehu_Mahdi
Asali: Twitter

Rahoton Daily Trust ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sanye da fararen kaya sun ɗauke shi daga asibitinsa da ke Unguwar Dosa, Kaduna, da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Laraba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahdi Shehu: Hukumomin tsaro sun yi shiru

Babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan kama ɗan gwagwarmayar kuma mai sharhi kan harkokin siyasa har kawo yanzu.

Sai dai, ɗansa, Buhari Mahdi Shehu ya bayyana cewa ba su samu jin ta bakin mahaifinsu ba ko ta wayar salula bayan kama shi a asibiti.

Buhari ya ce:

“Ba mu san ko kama shi aka yi ko gayyatarsa aka yi ba amma DSS sun zo sun tafi da shi daga asibitinsa da ke Unguwar Dosa a Kaduna, da misalin ƙarfe 11:00 na safe.”

Yadda jami'an tsaro suka kama Mahdi Shehu

A watan Disamba 2024, Mahdi Shehu ya fuskanci shari'a a kotu kan zargin wallafa bidiyon da ake cewa ya ƙunshi bayanai masu yaudarar jama’a a kafar sada zumunta.

Kotun jihar Kaduna ta bayar da belinsa a ranar 9 ga Janairu, 2025, kan kuɗi Naira miliyan 3 tare da kawo manyan malaman addini guda biyu da za su tsaya masa.

Kara karanta wannan

"Soyayya ruwan zuma": Saurayi ya bankawa budurwarsa wuta, ya ce zai aure ta

Mahdi Shehi ya godewa masoyansa

A cikin jerin saƙonni da ya wallafa a karshen mako, Mahdi ya gode wa magoya bayansa da suka nuna damuwa, addu’a, da goyon baya yayin da aka tsare shi na tsawon kwanaki 12.

Ya ce:

“Na gode wa waɗanda suka nuna damuwa, goyon baya, da addu’o’i yayin da aka tsare ni. Har wa yau, na gode wa waɗanda suka yi murna da wannan lamari, domin kun ƙarfafa ni da ƙara mani darasin duniya."

Ya kuma nemi afuwar rashin iya amsa sakonni sama da miliyan 4 a shafukan sada zumunta daban-daban da yake amfani da su.

Sai dai kwanaki kaɗan bayan haka, jami'an tsaro sun sake cafke shi a Kaduna duk da babu wata sanarwa a hukumance zuwa yanzu.

Yadda aka kama Mahdi Shehu a baya

Kun ji cewa jami'an tsaro sun taba cafke shahararren ɗan gwagwarmaya, Mahdi Shehu, wanda ya saba bankaɗo sirrin ƴan siyasa da shugabanni.

Kara karanta wannan

Kayayyakin miliyoyin naira sun kone bayan tashin gobara a fitacciyar kasuwa

Ɗan kasuwar wanda ke zaune a jihar Kaduna yana yawan sukar gwamnati da kuma tonon sililin da gwamnati take da ja da gaskiyarsu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262